Tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Tarayya, Yakubu Dogara, Ya Fice Daga APC Ya Koma PDP

Tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Tarayya, Yakubu Dogara, Ya Fice Daga APC Ya Koma PDP

  • Tsohon shugaban majalisar wakilai ta ƙasa, Yakubu Dogara, ya sauya sheka daga APC zuwa PDP
  • A ranar Jumu'a da ta gabata, Dogara da wasu shugabannin APC a arewa suka tabbatar da goyon bayansu ga Atiku
  • Lamarin bai zo da mamaki ba sakamakon yakin da suke da tikitin Musulmi da Musulmi wanda jam'iyyar APC ta tsayar

Lagos - Tsohon kakakin majalisar wakilan tarayyan Najeriya, Yakubu Dogara, ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki zuwa jam'iyyar PDP.

Jaridar Punch tace wannan na zuwa ne awanni 48 bayan Dogara, da wasu fusatattun jagororin APC a arewacin Najeriya sun ayyana goyon bayansu ga ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar.

Yakubu Dogara.
Tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Tarayya, Yakubu Dogara, Ya Fice Daga APC Ya Koma PDP Hoto: Punchng
Asali: UGC

Hakan ya biyo bayan zaman da kungiyar dattawan arewa ta yi tare da kusoshin APC mabiya addinin Kirista a arewa, daga ƙarshe suka yanke mara wa Atiku baya ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan

2023: Bola Tinubu Ya Ja Wa Kansa, Wani Babban Jigon APC Ya Fice Daga Jam'iyyar

A cewarsu, sun zaɓi Atiku ne bayan cimma matsaya tsakanin shugabannin Kiristoci na arewa da abokanan zamansu Musulmai na ɗaura ɗamarar yaƙar Tikitin masu addini ɗaya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma mai neman zama shugaban ƙasa a 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ne ya karɓi Dogara zuwa inuwar PDP a babban birnin kasuwanci, jihar Legas, Vanguard ta rahoto.

Sauya shekar Yakubu Dogara

Legit.ng Hausa ta gano cewa Yakubu Dogara, ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC ne a shekarar 2020.

Shugaban kwamitin rikon kwarya na APC ta ƙasa a wancan lokacin, gwamna Mala Buni na jihar Yobe ne ya sanar da ci gaban, inda yace shugaba Buhari ya yi murna da dawowar Dogara APC.

Haka zalika mun tattaro muku cewa Dogara, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki tare da wasu gwamnoni sun bar APC zuwa PDP a lokacin kakar zaɓen 2019.

Kara karanta wannan

2023: Jerin Sunayen Jihohin Arewa 6 da Fafatawa Zata Yi Ɗumi Tsakanin Atiku da Tinubu Tare da Dalilai

A halin yanzun da muke cikin 2022, bayan tabbatar da kudirin aiki tare da Atiku, Dogara bai tsaya nan ba ya tattara kayansa ya koma babbar jam'iyyar adawa ana shirin tunkarar 2023.

Ba Zan Zauna Gidan da Aka Lullube da Karya Ba, Jigon APC Ya Fice Daga Jam'iyyar

A wani labarin kuma Wani Jigon APC a jihar Kuros Riba, Ray Murphy ya ce ba zai cigaba da zama jam'iyyar da ake yawan sakin layi ba a bainar jama'a

Yace Najeriya na bukatar nagartaccen shugaban wanda ya zarce barkwanci subutar baki da APC ke kokarin kakabawa mutane a a zabe mai zuwa.

Idan baku manta ba tun bayan fara yakin neman zaben APC, Tinubu ya yi subutar baki a lokuta da dama kamar a Jos, jihar Filato da kuma Bayelsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262