Jiga-Jigan APC Sun Sauya Sheka Zuwa PDP, Gwamna Emmanuel Ya Tarbe Su
- Gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, ya kara jaddada cewa Atiku ne zabin da ya dace da shirin ceto Najeriya
- Manyan jiga-jigan jam'iyyar APC sun sauya sheka zuwa PDP a wurin wani biki da aka shirya a Uyo, babban birnin jihar
- Wannan na zuwa ne awanni kaɗan bayan jagorocin APC kiristoci a arewa sun mara wa Atiku baya
Akwa Ibom - Yayin da babban zaɓen 2023 ke kusantowa, gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom ya ƙara jaddada cewa PDP da Atiku Abubakar ne zaɓi mafi Alheri wajen ceto Najeriya.
Gwamnan, shugaban kwamitin yakin neman zaɓen Atiku/Okowa na kasa (PCC), ya faɗi haka ne yayin da yake jawabi a wurin wani taro a Uyo, babban birnin jiharsa.
Yace PDP na ƙara tara magoya baya yayin da ɗaruruwan masu sauya sheka bisa jagorancin ƙusoshin APC ke ci gaba da tururuwar sake dawowa jam'iyyar PDP a ƙarshen makon nan.
A cewarsa manyan jiga-jigan da suka haɗa da tsohon kakakin majalisar jiha, Nse Ntuen, tsohon mataimakin shugaban PDP, tsohon shugaban ƙaramar hukumar Uyo, waɗanda suka bi bayan tsohon gwamna, Godswill Akpabio, zuwa APC sun canza shawara.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Leadership ta rahoto cewa manyan ƙusoshin na jam'iyyar APC sun sake komawa asalin gidansu watau PDP a wani biki da aka shirya a Unity Park, Udo Udoma Avenue, Uyo.
Gwamna Emmanuel, wanda ya musu maraba da sauran masu sauya sheƙa daga jam'iyyu daban-daban, ya tabbatar musu da babu wanda zai nuna masu wariya a PDP.
Sai dai gwamnan ya gargaɗi masu shirin yi wa PDP zagon ƙasa inda ya jaddada cewa:
"Akwa Ibom da baki ɗaya shiyyar kudu maso kudu zasu fi samun tagomashi idan PDP ke kan karagar mulki a kowane mataki. Ina tabbatar muku babu zancen wai yanzu kuka dawo PDP, ku shiga sahu kawai an zama ɗaya."
Mambobin Jam'iyyar PDP da LP Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Jihar Nasarawa
A wani labarin kuma jam'iyyar APC mai mulkin jihar Nasarawa ta samu ƙarin magoya baya a yankin ƙaramar hukumar Nasarawa
Gwamna Abdullahi Sule ya nuna jin daɗinsa yayin da ya karbi tuban dubbannin masu sauya sheƙa daga manyan jam'iyyu kamar PDP da Labour Party.
Gwamnan ya tabbatar musu da cewa akwai haɗin kai mai kwari a APC kuma su ɗaukar tamkar suna cikin gidansu babu mai nuna musu banbanci.
Asali: Legit.ng