Kada Kuji Tsoron Zaben 2023 Osinbanjo Ya Fadawa Kirsitocin Nigeria
- Kungiyar Kiristocin Nigeria Ta Zargi Jam'iyyar APC Mai Mulki Da Maida Ta Saniyar Ware A Sha'annin Mulki
- Kungiyar Kiristocin Arewa Tayi Allah-Wadai Da Abinda Jam'iyyar APC tayi na zabar Dan takarar shugaban kasa Muslmi da musulmi
- Kungiyar Kiristocin Arewa Ta Marawa Atiku baya a zaben Shekarar 2023 a Matsayin Dan Takarar Shugaban Kasa
Abuja: Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce mabiya addinin kirista ‘yan Najeriya kar su ji tsoron zaben 2023.
Osinbajo, wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ya wakilta a taron bautar shekara-shekara ta 2022 a yammacin Lahadi a cibiyar Kiristoci ta kasa da ke Abuja.
Ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“ Taken da kuka dauka kan bikin bana shine: ‘Kada ku ji tsoro’. Wannan batu ne mai matukar muhimmanci ga kowannenmu duk da muna tunkarar shekarar 2023 kuma ake ganin kasar nan zata shiga tsaka mai wuya. To ina tabbtarwa da yan kasa kar suji tsoro kuma muna tare da mabiya addinin kirista kiristoci "
“Duk waɗannan batutuwa suna zuwa da tambayoyi da yawa, amma muna da tabbaci daga Ubangijinmu da Mai Cetonmu. Ba zai bar zukatanmu su firgita ba. Mu yi imani da shi kuma mu yi imani da Allah."
Jaridar The Nation ta rawaito cewa shugaban kungiyar kiristocin Najeriya CAN Archbishop Daniel Okoh ya ba da shawarar cewa kada tsoro ya sa ‘yan Najeriya su yanke hukunci ko kuma su yanke hukunci daga rahmara ubangiji.
Ya ce:
“Yayin da ‘yan Najeriya ke shirin tunkarar babban zabe a 2023, mutane da yawa ba su da tabbacin wanne irin sakamako za'a samu. Akwai fargabar cewa wasu na iya tayar da tarzoma idan zaben bai yi masu dadi ba. kamar yadda ake ganin wasu na‘yan kone-kone da lalata kayayyakin zabe a wasu wurare da tunanin lalata zaben 2023.
“Muna cikin wani mawuyacin hali saboda rashin tsaro ga rashin tabbacin mai nkan je yazo.
“Wadannan al’amura suna da ban tsoro da gaske amma ta yaya za mu canaja daga wannan yanayin da muka sami kanmu a ciki? Tsoro na iya haifar da kuskuren da ba za a iya gyarawa ba. Ya kamata mu rayu cikin tsoro? A’a, bai kamata mu ji tsoro ko da a fuskantar waɗannan ƙalubale ba.
“Kada mu bar tsoro ya hana mu yin yakar rashin adalci. A bar dukiyoyi da mukaman mulki a raba su cikin adalci a tsakanin al’ummomin kowane yanki da kabilu ba tare da barazana ga wanzuwar wata kabila ko addini ba, a’a, hakan zai taimaka mana wajen yin amfani da dimbin abubuwan da suke da shi a wannan kasa tamu don ci gaban kasa.
“Kada mu bari tsoron faduwa zabe ya kai mu cikin tashin hankali da magudi kafin zaben 2023 da lokacin da kuma bayan zaben. ’Yan siyasa su shiga yakin neman zabe da tunanin cewa bayan an yi kokari na gaske su kuma mika wuya ga Allah domin yanke hukunci na karshe.
“Kada mu bari tsoro ya kai mu ga jarabar yaudarar jama’a da ba su ji ba ba su gani ba, ta hanyar labaran karya. Dole ne shugabannin addini da na siyasa da kafafen yada labarai su samar da bayannai ga 'yan Najeriya masu inganci dan samu sakamako mai kyau.
Gabatar da Shettima: Kungiyar Kiristoci ta kalubalanci Tinubu da ya bayyana sunayen fastocin da suka je taron
Mabiya Addinin Kirista a Nigeria Masu kungiya CCCN sun zargi Jam'iyyar APC da tara malaman bogi wajen gabatar da dan takarar mataimakin shugaban kasa
A delilin haka kungiyar ta kalubalanci jam'iyyar da dan takarar jam'iyyar gabatar da sunayen malamn da suka halarci taron
Asali: Legit.ng