Gwamnatin Tarayya Ta Gargadi Gwamnoni Masu Amfani Da Yan Daba Don Tarwatsa Kamfen Din Abokan Hamayya
- Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi kakkausan gargadi ga gwamnonin jihohi
- Manjo Janar Babagana Monguno, ya bukaci gwamnoni masu amfani da yan daba wajen hana abokan hamayya kamfen su shiga taitayinsu
- NSA din ya ce an zuba jami'an tsaro domin yin maganin masu tarwatsa gangamin kamfen din abokan hamayya
Abuja - Gwamnatin tarayya ta gargadi gwamnoni masu amfani da yan daba da sauransu don hana abokan adawa gudanar da yakin neman zaben a jihohinsu da su janye daga hakan.
FG ta bayyana cewa hukumomin tsaro su tura jami’ansu domin kawo karshen wannan rashin hakurin, jaridar The Nation ta rahoto.
Za a dauki mataki kan wanda aka kama da hana abokan hamayya kamfen
Babban mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya ne ya yi wannan gargadin yayin taron ministoci na mako wanda tawagar labaran shugaban kasa suka shiya a fadar villa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Monguno wanda ya bayyana shirye-shirye da nasarorin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a ma’aikatar tsaro yana martani ne ga wata tambaya game da wani salo da aka fito da shi a jihohi.
Cewa gwamnoni sun dauki wasu matakai don muzgunawa tsarin yakin neman zaben abokan hamayya a siyasa a cikin alkaryarsu.
Monguno ya gargadi gwamnoni da su “saita yan kanzaginsu saboda idan muka yunkura, ba za su samu mafaka ba.”
Wannan gargadi na zuwa ne yan kwanaki bayan wani jigon PDP ya ci na jaki a wajen gangamin yakin neman zaben gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom saboda ya saka rigar Atiku Abubakar.
Buhari ya zargi gwamnoni da wawure kudaden kananan hukumomi
A wani labarin kuma, mun ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zargi gwamnonin jihohi da aikata rashawa ta hanyar wawure wani kaso daga cikin kudaden da ake warewa gwamnatocin kananan hukumomi.
Buhari wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 1 ga watan Disamba ya ce wannan abu da gwamnoni ke yi na nuna rashin gaskiya da kuma matakin da ayyukan cin hanci da rashawa ya kai a kasar.
Hakazlika shugaban kasar ya zargi wani gwamna da karbar kudade da sunan gwamnatin kananan hukumomi a jiharsa amma sai ya raba kudaden gida biyu ya baiwa ciyamomi rabin kudin kawai.
Asali: Legit.ng