Kotun Abuja Ta Ba Da Belin Shugaban Jam'iyyar APGA Na Kasa
- Babbar Kotun birnin Abuja dake zama a Bwari ta amince da bayar da belin shugaban jam'iyyar APGA, Chief Edozie Njoku
- A ranar Litinin da ta gabata Alkalin Kotun ya umarci a tasa keyarsa zuwa gidan gyaran hali kan tuhumar yi wa Kotun koli ƙarya
- Ana zargin Mista Edozie da buga takardar hukuncin Kotun koli ta karya tare da haɗin bakin shugaban matasan APGA, Chukwuemeka Nwoga
Abuja - Babbar Kotun birnin tarayya Abuja mai zama a Bwari ta amince da ba da Belin shugaban tsagin jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), Chief Edozie Njoku.
Mista Edozie tare da shugaban matasan jam'iyyar, Chukwuemeka Nwoga, an tasa su zuwa gidan gyaran Hali dake Suleja bisa umarnin mai shari'a Mohammed Madugu ranar Litinin.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa ana zargin jiga-jigan siyasar biyu da shirya takardar hukuncin Kotun Ƙoli ta bogi domin su ayyana kansu a matsayin shugaban APGA da shugaban matasa.
A rahoton jaridar Vanguard, bayan karanta musu abinda ake zarginsu da aikata wa, mutanen biyu sun musanta nan take.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kotu ta gindiya sharuddan Beli
Alkalin Kotun, mai Shari'a Madugu ya bayyana cewa laifin da ake zarginsu da aikata wa suna cikin irin waɗanda ake iya ba da Belinsu, amma ya gindaya sharuɗɗa.
Yace waɗanda ake zargin sai sun kawo wanda zai tsaya musu kuma wajibi ya zama ma'aikacin gwamnati wanda ya kai mataki na 15 a Albashi ko sama da haka kuma mazaunin birnin tarayya Abuja.
Ko kuma wanda zai tsaya musu ya kasance mamallakin wata kadara wacce ke da shaidar mallaka ta ainihi, inji Alkalin Kotun.
Kotu Ta Yanke Wa Mutumin da Aka Kama da Katin Zabe Sama da 100 Hukunci a jihar Sokoto
A wani labarin kuma hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa wato INEC tace Kotu ta yanke wa Nasiru Idris, wanda aka kama da Katunan zaɓe sama da 100 hukunci.
A cewar Festus Okoye, kwamishinan yaɗa labarai na hukumar INEC ta ƙasa, Kotun Majistire a Sokoto ta yanke masa zaman gidan yari na tsawon shekara ɗaya.
Bugu da kari, yace wanda 'yan sanda suka kama da PVC sama da 300 a jihar Kano na gaban Kuliya kuma zasu ci gaba da sa ido su ga hukuncin da za'a yanke masa.
Asali: Legit.ng