Majalisar Osun tayi Fatali da Bukatar Gwamna Adeleke na Sauya Sunan Jihar

Majalisar Osun tayi Fatali da Bukatar Gwamna Adeleke na Sauya Sunan Jihar

  • Majalisar dokokin jihar Osun, tayi watsi da bukatar Gwamnan jihar na sauya sunan jihar baki daya a yayin bikin rantsar dashi da aka yi
  • Majalisar tace, daga kan taken kasa, tambarinta har zuwa tutar kasa sun zama doka daga ranar 18 ga Disamban 2018 don haka ba zasu canzu ba
  • Sun jaddada cewa, sun fi son ma’anar farko ta jihar wacce ke nufin jiha mai nagarta a maimakon a canza ma’anarta mai kyau

Osun - Majalisar jihar Osun a ranar Litinin, ta fusata kan hukuncin sabon Gwamnan jihar, Sanata Ademola Adeleke na sauyawa jihar suna daga “State of Osun” zuwa Osun State.

Gwamna Ademola Adeleke
Majalisar Osun tayi Fatali da Bukatar Gwamna Adeleke na Sauya Sunan Jihar. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Jaridar The Cable ta rahoto cewa, majalisar ta musanta cewa taken jihar da tutarta duk an gina su ne da dokokin da aka amince dasu a ranar 18 ga watan Disamban 2012 kuma babu mutumin dake da karfin canzawa.

Jaridar Punch ta rahoto cewa, Adeleke yayin rantsar dashi a ranar Lahadi, 27 ga Nuwamban 2022 ya sauya sunan jihar daga “State of Osun” zuwa “Osun State” inda hakan ya sauya ma’anar sunan jihar.

Adeleke ya kwace dukkan nadin da tsohon Gwamna Adegboyega Oyetola yayi tun daga ranar 7 ga watan Yulin 2022, jaridar TheCable ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da bayar da umarnin daskarar da asusun bankunan jihar inda ya kara da cewa dukkan abinda Gwamnatin Oyetola tayi daga ranar 17 ga Yulin 2022 an soke su.

A martanin jihar kan hukuncin gwamnan, majalisar ta bakin shugaban kwamitinta na yada labarai, Moshood Kunle Akande, ya fitar da cewa majalisar ta saurari jawabin sabon gwamna wurin rantsarwa sun yanke hukunci kamar haka:

“Amfani da taken jiha, tambari da tuta duk sun ginu kan dokoki kuma don haka amfani dasu doka ne ba ra’ayi ba.

“Tabbatar da “taken State of Osun, tambari da tuta duk an yi su ne a ranar 18 ga Disamban 2012 wanda ke kunshe a sashi na 1, II, III, IV da V wanda a tsanake ya bada bayanin duk abinda dokar ta kunsa bashi da harshen damo.
“Na farko shi ne taken jihar, na biyu ya shafi tambari da na uku kuma tutar jihar.
“A karshe, mun san da hukuncin kotu a kan hakan.”

‘Yan Majalisar sun kara da cewa jihar zata cigaba da amsa sunanta na “State of Osun da kuma “Ipinle Omulabi” ma’anar a “Jiha tagari”.

Gwamba Adeleke ya kori ma’aikata 12,000

A wani labari na daban, Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya kori ma’aikatan jihar 12,000.

Bai tsaya nan ba, ya kara da tube rawunan sarakuna uku da tsohon gwamnan jihar ya nada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel