Kasa da Sa’a 24 da Hawansa Gwamna, Adeleke ya Fatattaki Ma’aikata 12,000 a Osun

Kasa da Sa’a 24 da Hawansa Gwamna, Adeleke ya Fatattaki Ma’aikata 12,000 a Osun

  • Sabon Gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya kori ma’aikata 12,000 na jihar kasa da sa’o’i 24 da rantsar dashi matsayin gwamna
  • Bai tsaya nan ba, ya tube rawunan sarakunan gargajiya uku na jihar inda ya umarci jami’an tsaro da su maye fadarsu yayin da suka tattara komatsansu
  • Sabon gwamnan ya kori manyan sakatarorin gwamnatin jihar 30 yayi da ya dakatar da shugabannin kananan hukumomi da hukumar zabe ta jihar

Osun - Kasa da sa’o’i 24 da rantsar da shi Gwamnan Jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke ya kori ma’aikata 12,000 kuma ya bukaci a tube rawanin sarakuna uku.

Gwamnan ya rushe nadin manyan sakatarorin Gwamnatin jihar 30 sannan ya dakatar da shugabannin kananun hukumomi da mambobin hukumar zabe mai zaman kanta na Jihar Osun, (OSIEC), jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Awanni Bayan Rantsar Da Shi, Sabon Gwamnan PDP Ya Yi Manyan Nade-Nade 3 Masu Muhimmanci

Sarakunan da lamarin ya shafa sun hada da Akirun din Ikinrun, Oba Yinusa Akadiri, Aree din Ire, Oba Ademola Oluponle da Owa din Igbajo, Oba Gboyega Famodun.

Sannan ya bukaci sarakunan da su tattara duk komatsansu su bar fada, yayin da ya bukaci jami’an tsaro da su maye gurbinsu.

A wata takarda wacce Sakataren watsa labaran Adeleke, Olawale Rasheed a ranar Litinin ya fitar, ya ce sabon gwamnan ya sanya hannu kan duk umarnin gwamnatin wadanda su ka hada da al’amuran sarauta, nade-nade, hada kwamitin dube-dube, binciken ma’aikata da kuma lamurran samar da aiki, jaridar The Nation ta rahoto.

Abinda takardar da ya fitar ta kunsa

Takardar da babban sakataren yada labarai na Adeleke, Olawale Rasheed ya fitarwa a ranar Litinin tace, sabon Gwamnan yasa hannu kan umarnin wanda ya hada da lamurran masarautu ne gargajiya, daukar aiki, kafa kwamitin bincike da sauransu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Jingine Siyasa, Ya Bayyana Mutumin Da Ya Cancanci Zama Shugaban Kasa a 2023

Takardar tace:

“Dukkan ayyukan da gwamnatin jihar Osun ta dauka a kowanne mataki a dukkan ma’aikatu, sassa da cibiyoyi bayan ranar 17 ga watan Yulin 2022 duk an soke su.
“Umarni na biyar kan lamurran masarautu da nada sarakunan gargajiya na jihar Osun bayan 17 ga watan Yulin 2022 duk an umarci a sake dubasu tare da bin ka’idoji da dokokin gargajiya da al’adun da suka shafi masarautu.

“A bangaren masarautar Ikirun wurin nadin Akirun, Aree na Ire da Owa na Igbajo, an bukaci a dakatar dasu.”

Tsohon gwamna ya dauka ma’aikata 12,000 da manyan sakataror 30 aiki

Tsohon Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola ya dauka ma’aikata 12,000 aiki tare da manyan sakatarorin gwamnati 30.

Takardar da sakataren gwamnatin jihar Osun, Tesleem Igbaleye ya fitar ta kara da bayyana dakatar da shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Osun, Segun Oladitan da mambobinsa.

Ortom yayi habaici ga El-Rufai

Kara karanta wannan

Da Duminsa: An Rantsar da Adeleke Gwamnan Osun na 6 a Tarihin Jihar

A wani labari na daban, Gwamna Ortom na jihar Binuwai yace takwaransa na jihar Kaduna bai isa yayi masa gori kan tsaro ba.

Gwamnan jihar Binuwai din yace kada El-Rufai na jihar Kaduna ya manta, korar ma’aikata dubu hudu yayi dare daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel