Shehu Ningi: Hadimin Buhari Ya Fara Zawarcin Jigon Jam'iyyar Su Kwankwaso Da Ya Fice

Shehu Ningi: Hadimin Buhari Ya Fara Zawarcin Jigon Jam'iyyar Su Kwankwaso Da Ya Fice

  • Jam'iyyar kayan marmari ta yi babban rashi na wani jigonta gabannin babban zaben 2023
  • Ma'ajin NNPP na kasa, Shehu Ningi ya sanar da sauya shekarsa daga jam'iyyar su Kwankwaso
  • Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya nuna farin ciki tare da fatan Ningi ya dawo tsohuwar jam'iyyarsa d

Mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari kan shafukan sadarwar zamani, Bashir Ahmad, ya yi murnar sauya shekar ma'ajin jam'iyyar NNPP na kasa, Shehu Ningi daga jam'iyyar.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Ningi, a cikin wata sanarwa mai kwanan wata 25 ga watan Nuwamban 2022, ya ce ya yanke shawarar sauka daga mukaminsa na ma'ajin jam'iyyar na kasa.

Har ila yau, dan siyasar ya kuma sanar da ficewarsa daga jam'iyyar ta su Kwankwaso saboda wani dalili nasa na kansa.

Kwankwaso
Shehu Ningi: Hadimin Buhari Ya Nuna Farin Cikinsa da Rashin Da Kwankwaso Ya Yi a NNPP Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Tsohon shugaban na NNPP a Bauchi ya kuma ce zai sanar da mataki na gaba da zai dauka da kuma jam'iyyar da zai koma a makon nan.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tinubu, Atiku, Obi, Da Wasu Suna Cikin Matsala Yayin Da INEC Ta Fitar Da Sabbin Ka'idoji

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Zagaye-zagayen da Shehu Ningi yayi tsakanin jam'iyyun siyasa

Ningi wanda ya kasance APC ya fice daga jam'iyyar sannan ya koma PRP kafin ya sake komawa APC kafin ya koma NNPP.

Lokacin da yake APC, ya yi kwanishinan kasafin kudi da tsare-tsare karkashin gwamnatin Mohammed Abubakar.

Ya yi murabus daga mukaminsa na kwamishina a ranar 23 ga watan Disambar 2016 bisa ikirarin cewa gwamnan ya mayar da shi saniyar ware.

Ya koma PRP inda ya zama shugaban jam'iyyar a jihar Bauchi. Amma a ranar 17 ga watan Oktoban 2020, Ningi a wata wasika zuwa ga shugaban PRP na kasa, Falalu Bello, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar.

Bayan sauya shekarsa daga PRP sai ya sake koma tsohuwar jam'iyyarsa ta APC.

Da alama APC za ta yi babban kamu

A wata wallafa da yayi a daren ranar Asabar, hadimin shugaban kasar ya nuna karfin gwiwar cewa Ningi zai sake dawowa APC.

Kara karanta wannan

Alkawari kaya: Tinubu ya fadi yadda zai yi da 'yan IPOB idan ya gaji Buhari a 2023

Ya rubuta:

"Ma'ajin NNPP na kasa, Shehu Barau Ningi, Shehu Barau Ningi, ya fice daga jam'iyyar. Muna fatan yi masa maraba zuwa jam'iyyarmu mai albarka, APC."

Allah ya baka lafiya, Dino Melaye ya yi martani ga barambaraman da Tinubu ya yi a wajen kamfen dinsa

A wani labarin, mun ji cewa kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar ya yi ikirarin cewa dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu na fama da cutar mantuwa.

Da yake masa addu'an samun lafiya, kakakin kwamitin, Sanata Dino Melaye ya zargi masu tura Tinubu ya nemi shugabancin kasar da yi masa mugunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng