Yadda Gangamin Tinubu Ke Gudana A Legas: "Ku Koya Wa Atiku Darasi Na Tarbiya", Tinubu Ya Fada Wa APC

Yadda Gangamin Tinubu Ke Gudana A Legas: "Ku Koya Wa Atiku Darasi Na Tarbiya", Tinubu Ya Fada Wa APC

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ya yi gangamin sa na zaben 2023 a jihar Legas a yau Asabar 26 ga watan Nuwamban 2022.

A wurin jagoran APCn na kasa, wannan gangamin shi ne mafi girma kuma ya zama tamkar bikin dawowa gida ne a gare shi bayan ya yi nasara a zaben fidda gwani na jam'iyyar da ke mulki a watan Yuni.

Bisa la'akari da girma da muhimmancin kamfen din, jam'iyyar APC ta aike da sanarwar shawarwari na zirga-zirga ga mazauna Legas a makon da ta gabata gabanin wannan ranar mai tarihi, don kaucewa cinkoso a titunan jihar.

Tuni dai wasu jiga-jigan APC sun fara isowa filin wasanni na Teslim Balogun, inda za a gudanar da gangamin na dan takarar shugaban kasar

Gangamin Tinubu
Uwar Dukkan Yakin Neman Zaben 2023: Yadda Ake Shirin Kamfen Din Tinubu A Legas
Asali: Original

Wadanda Legit ta hanga sun hada a ciyaman din APC na jihar Legas, Collenius Ojelabi, da direkta janar na kamfen din Legas, Sanata Ganiyu Solomon.

Gangamin Jagaban: Tinubu ya fara jawabi

Mutumin da aka taru saboda shi, Tinubu, ya fara jawabinsa da waka inda ya aike da gargadi ga abokan hamayyarsa.

Ya ce:

"Ina mika godiya ga Allah saboda bamu rai muka ga yau.
"Wannan juyin-juya hali ne na tsintsiya.
"Bana tunanin akwai abin da babu a nan a yau. Za mu cigaba da gwamnatin masu son kawo cigaba a 2023."

Ya ce Atiku ya na yin takara tun 1999 kuma yan Najeriya sun bashi dama a 2007.

Tinubu ya kara da cewa:

"Ina son in koya masa darasi na tarbiya a zabe da kuri'un ku.
"PDP ta yi shekaru 16 a kan mulki, ba su tuna da hanyar Badagry ba, da East-West road da sauransu.
"Butulu ne su. Kuna iya ganin dukkan gwamnonin mu a nan, suna tare da ni."

Shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Adamu ya yi jawabinsa

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adamu Abdullahi ya hau mimbari domin yin jawabinsa, ya ce Asiwaju Bola Tinubu ne shugaban kasa mai jiran gado.

Shugaban kungiyar gwamonin APC na kasa da NWC na jam'iyya sun hau mimbari don yin jawabinsu

Gwamna Bagudu na jihar Kebbi wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin APC ya bukaci al'umma su fito kwansu da kwarkwata su zabi Tinubu.

Ya ce dukkan gwamnonin APC 22 suna goyon bayan Tinubu dari bisa dari kuma sunyi imanin zai kawo alheri ga Najeriya.

Bagudu ya ce:

"Babu wani dan takarar shugaban kasa da zai iya tsayuwa kusa da Tinubu a batun cancanta da basira."

"Tinubu ne shugaban kasar Najeriya mai jiran gado" - Jawabin bude taro

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya iso wurin taron gangamin Tinubu.

A jawabinsa na bude taro, Gwamna Sanwo-Olu ya ce Tinubu ne shugaban Najeriya mai jiran gado.

Sanwo-Olu ya ce:

"Mun gode Asiwaju bisa bamu wannan madafar da muke ginawa a kai.
"Shine mutumin da ya fi dacewa a dukkan bangarori.
"Shine mutumin da zai iya kai Najeriya tudun na tsira.
"Ina son yi mana maraba zuwa birnin Asiwaju da kuma zuwa kwanku da kwarkwata."

Gbenga Daniel ya iso wurin gangamin na Tinubu

Tsohon gwamnan jihar Ogun, Otunba Gbenga Daniel ya iso wurin ganganin Tinubu

Isowar Gbenga Daniel
Uwar Dukkan Yakin Neman Zaben 2023: Yadda Ake Shirin Kamfen Din Tinubu A Legas
Asali: Original

Ana ta ihun 'Asiwaju' a yayin da magoya baya ke kokarin ganinsa

Ana ta ihu ana kiran sunan 'Asiwaju' a wurin taron a yayin da magoya baya ke kokarin ganin dan takarar shugaban kasar na APC

Daga karshe Tinubu ya iso wurin ganganin yakin neman zaben takarar shugaban kasar

Jami'an tsaro sun nuna kwarewar aiki a yayin da Jagaban ya iso filin wasanni na Teslim Balogun inda magoya baya suka dade suna jiran isowarsa.

Mutane sun kosa yayin da ake sa ran isowar Tinubu

Ana sa ran Asiwaju Bola Tinubu tare da tawagarsa za su iya wurin kowanne dakika daga yanzu inda ake gangaminsa na takarar shugaban kasa a filin wasanni na Teslim Balogun a jihar Legas.

Jaruman Nollywood sun iso domin kayyatar da wadanda suka hallarci taron da rawa da kide-kide

An maya da gangamin tamkar bikin kade-kade yayin da jaruman Nollywood suka fara kayyatar da magoya baya da baki da aka gayyata wurin da wakoki masu ban dariya.

Jaruman Nollywood
Uwar Dukkan Yakin Neman Zaben 2023: Yadda Ake Shirin Kamfen Din Tinubu A Legas
Asali: Original

Tsohuwar kakakin majalisar tarayya Patricia Olubunmi Etteh ta iso wurin taron

Tsohuwar kakakin majalisar dokokin tarayya, Patricia Olubunmi Etteh, yanzun ta iso wurin taron.

Gangamin Tinubu na Legas: Filin Wasanni na Teslim Balogun ya cika makil da magoya baya

Karin magoya baya da masoya suna shiga filin wasannin na Teslim Balogun inda ya kusa cika makil.

Mambobin majalisar dokoki na jihar Legas da yan kwamitin ayyuka NWC na APC a jihar sun isa wurin taron suna jiran isowar Asiwaju Bola Tinubu da shugabannin jam'iyyar na kasa.

Magoya Baya
Uwar Dukkan Yakin Neman Zaben 2023: Yadda Ake Shirin Kamfen Din Tinubu A Legas
Asali: Original

Legas za ta dau zafi

Joe Igbokwe, dan gani-kashe-nin Tinubu, a shafinsa na Facebook a ranar Asabar 26 ga watan Nuwamba, ya ce Legas za ta dau zafi saboda kamfen din Tinubu da aka dade ana jira.

Ya rubuta:

"Legas za ta yi zafi yau faaaa."
Kamfen Din Tinubu
Uwar Dukkan Yakin Neman Zaben 2023: Yadda Ake Shirin Kamfen Din Tinubu A Legas. Hoto: Joe Igbokwe
Asali: Facebook

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164