Gwamnan Babban Jiha A Arewa Ya Bayyana Yawan Shekarun Da Tinubu Zai Yi Kan Mulki Bayan Buhari
- Abdullahi Sule, gwamnan jihar Nasarawa ya ce Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC ne zai karba mulki daga Shugaba Buhari, ya yi shekaru 8
- Sule ya bayyana cewa babu dalilin kwatanta Bola Tinubu da sauran yan takarar domin yana gaba da su sosai
- Gwamnan na Nasarawa ya kuma ce danyen man da Najeriya ke hakowa da wasu abubuwa a kasar duk za su inganta karkashin mulkin Tinubu
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Bola Ahmed Tinubu, zai mulki Najeriya tsawon shekaru takwas, rahoton Daily Trust.
Ya kuma ce babu dalilin kwatantan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, da Tinubu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Gwamna Sule ya bayyana hakan ne yayin hirar da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Television.
Ya ce:
"Tattalin arzikin Legas a yau ya fi na jihar Anambra. Eh ko a'a. Tamkar dare da rana suke. Ka san ba a kwatantawa. Da ka ce in kwatanta su, menene ka ke so in kwatanta?"
Man fetur da Najeriya ke fitarwa zai karu karkashin Tinubu - Sule
Amma, gwamnan ya ce danyen man fetur da Najeriya ke samarwa zai karu kafin Shugaba Muhammadu Buhari ya bar mulki.
Ya ce:
"Yau duk matsalolin da muke fuskanta, muna samar da gangan mai miliyan 1.2 zuwa 1.3 ne duk rana. Lokacin da Muhammadu Buhari zai mika mulki ga Asiwaju, zai kasance ganga miliyan 1.5 ne duk rana.
"Za ka ga abin da ke faruwa a kasar nan. Hauhawar farashin kayayyaki zai ragu zuwa lamba daya da izinin Allah kuma sauran abubuwan za su bi sahunsa. Tinubu zai mulki kasar nan na wani shekaru takwas da izinin Allah."
APC Ba Za Ta Ci Zaben Shugaban Kasa Ba Saboda Tikitin Musulmi Da Musulmi - Babachir Lawal
A wani rahoton, Babachir David Lawal, Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, , ya ce cewa jam’iyyarsa ta APC ba za ta ci zaben shugaban kasa na 2023.
Babban jigon na APC ya ce Bola Ahmed Tinubu ba zai yi ci zaben mai zuwa ba don zaben Kashim Shettima musulmi dan uwansa da yayi a matsayin abokin takara, BBC ta rahoto.
Bababchir ya yi ikirarin cewa sun yi iya kokarinsu domin ganin Tinubu, wanda Musulmi ne ya samu tikitin jam’iyyar amma daga bisani sai suka gano cewa ya yi masu shigo-shigo ba zurfi ne a kan wanda zai dauka matsayin mataimakinsa.
Asali: Legit.ng