Kotun Daukaka Kara Ta Soke Zaben Fidda Gwanin Gwamnan PDP a Zamfara
- Kotun daukaka kara ta tabbatar koran dan takarar gwamnan PDP na jihar Zamfara, Dauda Lawal
- A baya kotun tarayya ta soke zaben fidda gwanin PDP da aka gudanar tare da umartar yin sabon zaben
- An sake zabe, Dauda ya sake samun nasara, amma batun ya kara komawa gaban kotu saboda wasu dalilai
Jihar Sokoto - Kotun daukaka kara mai zamanta a jihar Sokoto ta yi watsi da karar da PDP ta daga game da soke zaben fidda gwanin gwamnan da aka gudanar a jihar Zamfara.
Hukuncin kotun karkashin jagorancin mai shari'a Muhammad Shuaibu ya jaddada soke Dauda Lawal a matsayin dan takarar gwamnan PDP a jihar, Punch ta ruwaito.
Mai shari'a ya ce, daukaka karar da PDP ta yi bai da makama don haka ilahirin alkalan kotun sun amince da tabbatar da hukuncin baya.
Shuaibu ya kuma yi karin haske da cewa, Lawal bai da hurumin daukaka kara kan hukuncin da dama ya amince dashi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Hakazalika, kotun ta umarci PDP ta ba da tarar N100,000 bisa bata lokacin kotu, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.
Yadda lamarin ya faro
A tun farko, dan takarar gwamna a PDP, Ibrahim Shehu ya kalubalanci Lawal a nasarar da ya yi a zaben gwamnan da aka gudanar.
Shehu ya dage cewa, an murdiya a zaben fidda gwanin da aka gudanar tare da saba ka'idojin zabe da INEC ta shar'anta.
Ganin bai gamsu da zaben ba, ya tunkari kotun tarayya mai zama a Gusau, ita kuwa ta rusa zaben tare da ba da umarnin a sake shi cikin kwanaki 14.
PDP ta amince da hukuncin kotun, ta sake gudanar da zaben da Lawal ya sake lashewa.
Har ila yau, Shehu ya sake tunkarar kotun ta tarayya, inda ya shaida cewa, babu wani zabe da aka yi dashi, kuma PDP bata da dan takarar gwamna a Zamfara a 2023.
Da yake martani ga hukuncin da aka yanke yau, lauyan wanda ya daukaka karar Aminu Aliyu ya shaida cewa, wanda yake karewa na da damar daukaka kara zuwa kotun koli.
Shi ma da yake jawabi, lauyar wanda ake kara, Ndiana Anaka ta ce wannan hukuncin nasara ce mulkin dimokrardiyya.
A baya kotu ta soke irin wannan zabe na fidda gwani a jihar Ogun tare da umartar sake sabon a gaba.
Asali: Legit.ng