Gwamnan Katsina Ya Zubda Hawaye Yayin Gabatar da Kasafin Kuɗinsa Na Karshe
- Gwamnan Katsina ya gaza rike kansa ya zubar da hawaye a zauren majalisar dokokin lokacin da yake gabatar da Kasafin kuɗin 2023
- Aminu Bello Masari ya yi hawaye ne a lokacin da yake bayanin Kasafin ya yi ƙasa idan aka kwatanta da na bara
- Masari, tsohon kakakin majalisar wakilan tarayya ya zama gwamnan Katsina ne a shekarar 2015, ya sake zarcewa a 2019
Katsina - Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya zubar da hawaye yayin gabatar da Kasafin kuɗin gwamnatinsa na ƙarshe a majalisar dokokin jihar ranar Talata.
Jaridar Channels tv tcae Kasafin Kudin ya ƙunshi, "Kasafin shirye-shiryen miƙa mulki," wanda zai laƙume Biliyan N288.63bn.
Ƙunshin kasafin na hekarar 2023 ya ware Kashi 63.77 cikin ɗari a ɓangaren manyan ayyukan jari da kashi 36.23 ga harkokin yau da kullum.
A cewar gwamna Masari, an tsara Kasafin ta yadda za'a ƙarisa ayyukan da gwamnati ke kan yi wa al'umma da kuma ƙirƙiro wasu sabbin ayyukan raya ƙasa da za'a iya kammala kafin karewar wa'adi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ayyukan dai zasu kewaye ɓangarorin Ilimi, Lafiya, samar da ruwa, noma da kiyo, kula da mahallai, hanyoyi, manyan ayyukan ci gaɓa da sauransu.
Meyasa gwamnan ya zubda hawaye?
Hawaye sun zubo daga idanun Masari ne lokacin da yake bayanin cewa Kasafin 2023 idan aka kwatanta ya yi ƙasa da Kasafin 2022 da kimanin Biliyan N34bn.
Masari, tsohon shugaban majalisar wakilan tarayya ta zama zababben gwamnan jihar Katsina ne a shekarar 2015 karkashin inuwar jam'iyyar APC.
Haka zalika Katsinawa sun sake zaɓensa ya zarce zango na biyu a babban zaben 2019, wa'adin mulkinsa zai ƙare ne a watan Mayu, 2023.
A wani labarin kuma Gwamnan Jihar Ebonyi Na APC ya gabatar da muhimmiyar bukatar Tinubu a gaban gwamna Wike na Ribas
Gwamna Dave Umahi yace ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar APC ba ya bukatar tallafin kayan yakin neman zaɓe daga wurin Wike.
A cewarsa, Tinubu na bukatar kafatanin kuri'un al'ummar jihar Ribas ne, ya roki gwamna Wike ya taimaka wa APC a zaben shugaban kasa kaɗai.
Asali: Legit.ng