Da Dumi-dumi: Hawaye Sun Kwaranya Yayin da APC Ta Rasa Dan Majalisarta a Plateau
- Dan majalisa mai wakiltan mazabar Qua’an Pan ta arewa a majalisar dokokin jihar Plateau ya kwanta dama
- Allah ya karbi ran Eric Dakogol wanda dan jam’iyyar APC ne a ranar Litinin bayan ya shafe makonni yana jinya
- Shugaban masu rinjaye a majalisar jihar ta arewa, Daniel Naanlong, ya tabbatar da mummunan labarin
Plateau - Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta rasa daya daga cikin yan majalisarta a jihar Plateau, Honourable Eric Dakogol, a ranar Litinin, 21 ga watan Nuwamba.
Kamar yadda gidan talbijin na AIT ta rahoto, Dakogol ya mutu ne bayan yar gajeruwar rashin lafiya a garin Jos, babban birnin jihar.
Ya yi jinya na dan lokaci kafin mutuwarsa, majiya
Kafin mutuwarsa, dan majalisar shine mamba mai wakiltan mazabar Qua’an Pan ta arewa a majalisar dokokin jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar wata majiya ta kusa da shi, Dakogol ya dauki tsawon wasu makonni yana jinya kafin Allah ya dauki ransa.
Koda dai shugabancin majalisar dokokin jihar Plateau bai riga ya bayar da wata sanarwa kan lamarin ba a hukumance, shugaban masu rinjaye, Daniel Naanlong, ya tabbatarwa gidan talbijin din da batun mutuwar Dakogol ga manema labarai.
Tsohon ministan noman Najeriya, Mustapha Shettima ya kwanta dama
A wani labari makamancin wannan, mun kawo a baya cewa Allah ya amshi ran tsohon ministan noma, tsaro da kuma harkokin cikin gida, Dr Shettima Mustapha a ranar Alhamis, 17 ga watan Nuwamba.
Babban jigon siyasar kasar ya rasu ne a babban birnin tarayya Abuja inda aka yi jana'izarsa a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno daidai da koyarwar addinin Islama.
Kafin mutuwarsa, Shettima ya bayar da gagarumin gudunmawa wajen ci gaban kasar musamman a bangaren bunkasa harkar noma wanda yana daya daga cikin abubuwan da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta baiwa muhimmanci.
Da yake fitar da wata sanarwa game da rashin Shettima, shugaban kungiyar manoman Najeriya (AFAN), Arc. Kabir Ibrahim ya bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi a garesu dama kasa baki daya.
A wani labari na daban, yan bindiga sun farmaki garuruwa hudu a kananan hukumomin Zurmi da Maradun da ke jihar Zamfara inda suka yi garkuwa da mutane fiye da 100 wadanda yawancinsu mata ne da yawa.
Asali: Legit.ng