Ba Zan Iya Yin Fushi da ESN Ba Saboda Ban Tabbatar da Wanda Ke Yin Laifin Ba
- Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour ya bayyana cewa, ba zai yi Allah-wadai da 'yan kungiyar ESN ba
- Peter Obi ya ce zai tattauna da wadanda ke kokarin ballewa daga Najeriya saboda wasu dalilai
- Kungiyar ESN na daga cikin kungiyoyin da ke addabar 'yan Najeriya da ayyukan ta'addanci, musamman a Kudu maso Gabas
Najeriya - Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour ya ce ba zai iya yin Allah-wadai da kungiyar ta'addanci ta ESN ba saboda bai san ya ayyukansu suke ba, TheCable ta ruwaito.
Tsohon gwamnan na Anambra ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wata tattauna da aka yi dashi, inda ya ce dukkan kungiyoyin aware na bore ne saboda gazawar shugabanci.
Ya bayyana cewa, idan aka zabe shi ya gaji Buhari a zaben 2023, gwamnatinsa za ta tsiri tattauna don warware matsalolin aware.
A kalamansa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Na farko a manufofinmu 7 shine tabbatar da tsaro rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya, kuma a nuna dunkulalliyar Najeriya guda daya ta hanyar daidaito, adalci, da kuma yin abu daidai da tafarkin doka.
"Ko'ina a kasar nan a cike yake da bore. Hakan ya samo asali ne ga gazawar shugabanci. Ba laifi bane yin bore. Tattaunawa za ku yi da kowa don sanin bakin zaren.
"Ba zan yi Allah-wadai da ESN ba saboda ban san wa ke yin wani ba. Za ka iya yin Allah-wadai da mutane ne idan akwai ma'aunin da ke nuna wannan mutumin ya yi wani abu."
Gwamnonin Kudu ne suka kirkiri ESN don cimma wata manufa, inji Obi
A bangare guda, Peter Obi ya ce gwamnonin yankin Kudu maso Gabas ne suka kirkiri kungiyar ta'addanci ta ESN don cimma wata manufa tasu.
Sai dai, jaridar TheCable ta ce ta bincika ta gano maganar Obi ba gaskiya bane.
A cewar jaridar, shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu ne ya ayyana kirkirar ESN a watan Disamban 2020.
A ranar 13 ga watan Disamban 2020, Kanu ya kaddamar ESN tare da cewa, aikin kungiyar shine kare al'ummar yankin Kudu maso Gabas daga barnar 'yan ta'adda.
A baya dama Peter Obi ya ce kungiyar IPOB, uwa ga ESN ba kungiyar ta'addanci bane duk da kuwa gwamnatin Buhari ta ayyana ta cikin tsageru.
Asali: Legit.ng