Na Kusa Da Wike Ya Jingine Tafiyar G5, Ya Halarci Gangamin Atiku Abubakar a Gombe
- Tsohon gwamnan Gombe kuma ɗan tafiyar tsagin Wike, Ibrahim Ɗankwambo, ya baiwa mutane mamaki a taron Atiku na jihar
- Ɗankwambo, ɗaya daga cikin mambobin G5 na sahun gaba, ya ba da tallafin motoci 20 ga yakin zaɓen Atiku/Okowa
- Tsagin gwamnan Ribas sun kafa sharaɗin cewa har sai Ayu yayi murabus zasu taya PDP kamfen shugaban kasa a 2023
Gombe - Tsohon gwamnan jihar Gombe kuma makusancin gwamnan Ribas, Nyesom Wike, watau Ibrahim Hassan Dankwambo, ya jingine tafiyar G5 da ake wa laƙabi da tafiyar gaskiya.
Leadership ta ruwaito cewa Dankwambo na ɗaya daga cikin fitattun mambobin tsagin Wike, waɗanda suke takun saƙa da shugabancin PDP da ɗan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar.
Tawagar G5 sun raba gari da Atiku ne bisa ci gaba da zaman Dakta Iyorchia Ayu a kujerar shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, sun ce ba gudu ba ja da baya sai ya yi murabus.
Haka nan kuma Gwamna Wike ya zargi Ayu, ɗan asalin jihar Benuwai, da karkatar da wasu kuɗaɗen da PDP ta tara daga sayar da Fam zuwa Aljihunsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan haka, mambobin tawagar Wike sun janye daga kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku/Okowa har sai Ayu ya sauka.
Makusancin Wike ya halarci Kamfen Atiku
Sai dai wani abu da yazo wa kowa da mamaki shi ne, tsohon gwamnan Gombe ya bi sahun Atiku da sauran ƙusoshin PDP da yammacin Litinin zuwa wurin gangamin kamfe.
An hangi Ɗankwambo a filin jirgin sama na Gombe yana maraba da manyan jiga-jigan PDP zuwa jihar Gombe da gangamin taron, ya kuma yi amfani da damarsa wurin jawabi ga magoya baya.
Jagoran gangamin Sanata Dino Melaye ya sanar da mahalarta gangamin cewa Ɗankwambo ya ba da kyautar motocin Bas 20 ga kwamitin yakin neman zaɓen Atiku/Okowa.
A wani labarin kuma Manyan yan takarar shugaban kasa biyu sun tara dandazon mutane a wuri daban-daban a jihar Delta
Magoya bayan APC sun cika fili maƙil yayin da suka tarbi ɗan takarar shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da 'yan tawagarsa ranar Asabar.
Haka zalika an ga mutane sun yi cikar kwari a wurin gangamin yakin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, duk a rana ɗaya.
Asali: Legit.ng