Wike Ya Tona Kudin da Buhari Ya Rabawa Jihohi, Gwamnonin Kudu Sun Shiga Runtsi
Gwamna Nyesom Wike ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta biya jihohin Neja-Delta wasu kudinsu
Akwai kason 13% da ake warewa Jihohin masu arzikin fetur, wanda Gwamnoni suke bin gwamnatin tarayya
Bayan Wike yace an biya wannan kudi, an fara tambayar abokan aikinsa abin da suka yi da kason jihohinsu
Rivers - Tambayar da jama’a suke yi a halin yanzu shi ne ina jihohin Neja Delta suka kai bashin rarar arzikin man fetur da gwamnatin tarayya ta biya su.
The Nation ta kawo rahoto cewa biyo bayan jawabin da ya fito daga bakin Gwamna Nyesom Wike a makon jiya, mutane sun taso gwamnonin Kudu a gaba.
Mai girma Gwamna Nyesom Wike ya shaidawa Duniya Gwamnatin Muhammadu Buhari ta dawowa Ribas kudin da take bi bashi na kason fetur din ta.
Gwamnan na Ribas yace da wadannan makudan kudi ne ya gudanar da ayyukan a zo-a gani. Daga ciki har da katuwar makarantar horas a Lauyoyi da ya gina.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ganin yadda Ribas ta ci moriyar kudin nan, masu ruwa da tsaki sun nemi sauran Gwamnonin da ke da arzikin fetur suyi bayanin inda suka kai na su kaso.
Amsar Gwamnatin Delta
Da aka tuntubi, Gwamnatin Ribas, Ifeanyi Okowa yace N30bn kadai suka iya karba daga N270bn da suke bin bashi a asusun kasonsu na rarar arzikin fetur.
Gwamnan ya yi bayani ta bakin babban sakataren yada labarasa, Olisa Ifeajika, yace tuni sun yi wa talakawa bayani suna bin N270bn daga 2010 zuwa yau.
A saurare mu - Bayelsa
Mutanen jihar Bayelsa sun nemi gwamnansu ya yi masu bayanin abin da yake jawo koma-baya a jihar duk da irin kudin da suke samu daga danyen fetur.
Da aka nemi Kwamishinan yada labarai na jihar Bayelsa, Ayibaina Duba, domin ya yi karin-haske a kan lamarin, jaridar tace bai iya daukar duk kiran waya ba.
Maxwell Ibiba wanda shi ne kwamishinan yada labarai ya yi alkawarin zai yi bayanin gaskiyar lamarin a yau. Har zuwa yanzu, ana sauraron bayaninsa.
A binciki Akwa Ibom - PAP
Babban jami’in tsarin PAP na kasa, Imoh Okoko ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta binciki inda aka kai kudin da ta biya jihohin, musamman a Akwa Ibom.
Okoko yace duk da dukiyar jihohin yankin suke da shi, babu cigaban kirki da za a iya nunawa a yankunan Eket, Ibeno, Eastern Obolo, Mbo, Ikot Abasi da Esit Eket
Alakar Najeriya-Kanada
A yau aka ji labari Mai magana da yawun Mataimakin Shugaban kasa, Laolu Akande yace Yemi Osinbajo zai kafa tarihin ziyartar Kanada, a karon farko bayan 2000.
Kafin ziyarar Farfesa Osinbajo, rabon da wani Shugaban Najeriya ya je kasar, tun zamanin Cif Olusegun Obasanjo wanda ya rike Najeriya tsakanin 1999 da 2007.
Asali: Legit.ng