Tsohon Sarki Sanusi II Ya Fadawa ‘Yan Najeriya Wadanda Ya Dace a Zaba a 2023

Tsohon Sarki Sanusi II Ya Fadawa ‘Yan Najeriya Wadanda Ya Dace a Zaba a 2023

  • Muhammad Sanusi II ya yi jawabi a kan shugabanci a wajen wani taron maulidin Annabi SAW a Abuja
  • Ustaz Muhammad Awwal Olohungbebe ya wakikci tsohon Sarkin Kano, ya gabatar da jawabinsa
  • Khalifa ya yi bayani a kan shugabanci a doron Islama, yace ana bukatar wadanda za su kamanta adalci

Abuja - Ganin babban zabe ya gabato a Najeriya, Mai martaba Malam Sanusi Lamido Sanusi ya yi kira ga jama’a a kan abin da ya shafi zaben 2023.

A wani rahoto da muka samu daga Daily Trust, tsohon Sarkin na Kano ya yi kira ga ‘Yan Najeriya da su zabi shugabanni masu nagarta da hangen nesa.

Muhammadu Sanusi II ya fadawa al’umma cewa su hada da addu’a wajen zaben jagororinsu. Sanusi II bai kama sunan wani ko wata jam'iyya ba.

Kara karanta wannan

2023: Ku Yi Hattara Da Peter Obi, Kungiyar Matasan Kirista Ta Aike Da Sako Mai Karfi Ga Yan Najeriya

Mai martaba ya yi wannan jawabi ne a ranar Lahadi, 20 ga watan Nuwamba 2022 a wajen wani bikin maulidin Annabi Muhammad (SAW) a Abuja.

Gidauniyar Ashraaf Islamic Foundation ta shirya taron maulidi na musamman, inda aka zanta kan abin da ya shafi shugabanni a mahangar musulunci.

Ustaz Olohungbebe ya wakilci Khalifa

Rahoton yace Ustaz Muhammad Awwal Olohungbebe na jami’ar jihar Kwara da ke garin Malete, shi ya samu wakiltar Sarkin Kano na 14 a wajen taron.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tsohon Sarki Sanusi II
Muhammadu Sanusi II yana karatu Hoto: @MSII_dynasty
Asali: Twitter

Ustaz Muhammad Awwal Olohungbebe a madadin Mai martaba, yace Musulunci zai cigaba da samun ta-cewa a kan harkar siyasa da jagoranci jama’a.

Duk da Najeriya ba kasar shari’a ba ce, Sanusi II yace bai dace da Musulmai su aikata wani abin da ya sabawa koyarwar littafin Al-Kur’ani da Hadisai ba.

Tsohon gwamnan na bankin CBN yace dole ne a samu Musulmai da za su yi zabe da wadanda za a zaba. A cewarsa ana neman nagarta da hangen nesa.

Kara karanta wannan

Majalisar Malamai da Limamai sun fito da ‘Dan takaran Shugaban Kasarsu a Zamfara

A madadin Khalifan Tijjaniya na Najeriya, Uztazun yake cewa ana bukatar Musulmai a kan mulki wadanda za suyi wa daukacin jama’a adalci da gaskiya.

Sharafudeen Abdulsalam Aliagan ya yi magana

Wanda ya assasa gidauniyar Ashraaf Islamic Foundation, Dr. Sharafudeen Abdulsalam Aliagan, ya gabatar da jawabi a taron maulidin da aka shirya.

An rahoto Sharafudeen Abdulsalam Aliagan yana cewa Musulunci bai kawowa damukaradiyya cikas, sai ma dai akwai inda addinin ke karfafar tsarin.

Wa Aisha Buhari take goyon baya?

An samu labari kwamitin neman takarar Bola Tinubu a APC ya yi magana bayan bidiyon Aisha Buhari ya bayyana tana tallata gwaninta a zaben 2023.

Shakka babu Aisha Buhari tana goyon bayan takarar Bola Tinubu da Kashim Shettima a APC, har an ga ta dankara wani kunshi mai kyawu a jikinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng