Tattakin Matasa Miliyan: Tinubu Ya Riga Ya Lashe Kuri'un Kano, Ganduje

Tattakin Matasa Miliyan: Tinubu Ya Riga Ya Lashe Kuri'un Kano, Ganduje

  • Matasa sun mamaye Titunan Kano yayin da suka fito tattakin nuna goyon baya ga ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar APC
  • Matasan sun fara tattakin ne daga fadar Sarkin Kano kana suka kare a gidan gwamnatin jihar ranar Lahadin nan
  • Gwamna Abdullahi Ganduje yace bisa ganin wannan cincirindo, Tinubu ya lashe zaɓen Kano ya gama

Kano - Dubbannin matasa sun yi cincirindo a Titunan jihar Kano ranar Lahadi domin nuna goyon bayansu ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa matasan sun fara tattakin ne daga Fadar mai martaba Sarkin Kano zuwa gidan gwamnatin jiha, daga nan kuma suka shiga taro.

Matasan Kano.
Tattakin Matasa Miliyan: Tinubu Ya Riga Ya Lashe Kuri'un Kano, Ganduje Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Twitter

A wurin taron mai taken, "Tattakin Miliyan ɗaya domin Tinubu," karkashin jagorancin jagoran magoya bayan Tinubu, Baffa Babba Ɗanagundi, ya samu haɗin kan matasa daga kananan hukumomi 36, sun halarci wurin.

Kara karanta wannan

Ana Tsaka da Shan Soyayya, Budurwa Ta Burma Wa Saurayinta Sadiq Ɗahiru Wuka Har Lahira

Da yake jawabi a wurin gangamin taron, gwamna Abdullahi Umar Ganduje, yace ganin wannan cikar kwarin na matasa, alama ce ta zahiri dake nuna Tinubu ya cinye Kano a zaɓe mai zuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Tinubu ya riga ya lashe kuri'un Kano kuma zai lashe zaɓen Najeriya insha Allahu. Muna tabbatar muku jam'iyyarmu a dunkule take kuma ta shirya tsaf babu wata taƙaddama a cikin gida."
"Muna tabbatar muku za'a yi sahihi kuma gamsasshen zaɓe a Kano, ba tada jijiyoyin wuya, ba faɗa ba saɓani kuma muna tattauna wa da sauran jam'iyyu don yin kamfe mai tsafta."

- Gwamna Ganduje.

Gwamna Ganduje ya ƙara da cewa nan ba da jimawa ba gwamnatinsa zata shirya liyafar cin abinci ta gayyaci baki ɗaya masu neman takarar gwamna jihar a 2023. Kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Magoya Baya da Makusantan Jonathan Sun Yanke Shawara, Sun Faɗi Wanda Suke So Ya Gaji Buhari a 2023

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa yau Lahadi bisa jagorancin ɗan Bola Tinubu, matasa suka gudanar da tattakin tabbatar da mubaya'arsu ga ɗan takarar na APC.

Tinubu da Peter Obi sun gudanar da kamfe rana ɗaya a Delta

A wani labarin kuma Hotunan Yadda Manyan 'Yan Takarar Shugaban Kasa Biyu Suka Tara Jama'a Ba Masaka Tsinke a Jiha Ɗaya

A wurare biyu daban-daban, magoya baya sun cika wurin kamfen Bola Tinubu na APC da takwarsan na jam'iyyar LP, Peter Obi.

Hotuna sun nuna yadda kowanen su ya samu kyakkyawar tarba daga dubbanin mutane a jihar Delta, kudu maso kudancin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262