Da Wahala Mu Ci Zabe Idan Har Ba Ayi Abubuwa 2 ba Inji Tsohon Gwamnan PDP
- A hasashen Ayodele Fayose, zai yi wahala jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar su iya kai labari a 2023
- A hirar da aka yi da shi, Ayo Fayose yace akwai bukatar PDP ta dinke barakar cikin gida da ‘Yan G5
- ‘Dan siyasar ya bada shawarar a sasanta da Peter Obi, wanda yake ganin zai bata ruwa, ba zai sha ba
Abuja - Ayodele Fayose wanda ya yi Gwamna har sau biyu a jihar Ekiti, yana ganin Labour Party (LP) za ta kawowa jam’iyyar PDP tasgaro a zaben 2023.
Da aka tattauna da shi a gidan talabijin na Channels TV a ranar Alhamis, 17 ga watan Nuwamba 2022, Ayodele Fayose ya yi bayani a kan halin siyasar kasa.
Fayose ya nuna da wahala Peter Obi wanda shi ne ‘dan takaran jam’iyyar LP ya zama shugaban kasa, amma yana ganin zai nakasa damar da PDP take da shi.
‘Dan siyasar yace ba dole ba ne Obi ya samu akalla 25% na kuri’u daga biyu bisa ukun jihohin da ke kasar nan kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Abubuwa 2 da za ayi - Fayose
The Cable ta rahoto Fayose yana cewa ya kamata jam’iyyar hamayya ta PDP ta sasanta da Obi, kuma ta shawo kan rikicin cikin gidan da ya dabaibaye ta.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tsohon gwamnan yana ganin nasarar PDP tana ga yin sulhu da jam’iyyar adawa ta LP, sannan kuma a dinke barakar Atiku Abubakar da su Nyesom Wike.
Hadarin Peter Obi
“Obi hadari ne da ya kamata ayi hattara da shi. Ba na tunanin zai samu kashi 25% na kuri’un biyu bisa ukun jihohin tarayya.
Ba na yi wa Obi adawa. Ina kaunarsa kuma tsayayyen shugaba ne shi. Amma bana tunanin zai samu 25% na kuri’un zabe.
Bari in ce Obi karfen kafa ne ga jam’iyyar PDP, babu maganar musanya wannan."
- Ayo Fayose
Fayose ya fadawa Channels cewa wannan hasashen ne kurum wanda ba dole ba ne ya tabbata, domin babu wani abin da zai yiwu a wajen Ubangiji ba.
Gaskiya ba ta da dadi
“Bari in yi maka fashin baki, a Kudu maso yamma, mutane ba su son a fada, ban ga ta yadda PDP za ta ci zabe ba. Mai yaudarar mu ya yi tayi.
Ban ga ta yadda PDP za ta ci Kudu maso gabas ba, Abubuwa da yawa za su faru a Kudu maso Kudu. Sai kuma muhimman jihohin da ke Arewa.”
- Ayo Fayose
A hirar da aka yi da shi, Fayose yace Rabiu Kwankwaso kan shi wata matsala ce ga PDP, domin zai dauke wasu kuri'un da ke jihohin Arewacin kasar.
Alakar Wike da LP
A duk lokacin da Peter Obi ya zo yin kamfe domin tallata jam'iyyar LP a jihar Ribas, an ji labari Gwamna Nyesom Wike yace zai ba shi goyon baya.
Alamu na nuna Mai girma Nyesom Wike bai da niyyar taimakawa Atiku Abubakar a halin da ake ciki, ya sha alwashintallafawa takarar Obi a zabe.
Asali: Legit.ng