Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwani, Ta Bayyana Halastaccen Dan Takarar APC a Jigawa

Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwani, Ta Bayyana Halastaccen Dan Takarar APC a Jigawa

  • Kotu ta soke zaben fidda gwanin jam'iyyar APC na dan majalisa mai wakiltan mazabar Kazaure ta jihar Jigawa
  • Mai shari'a Hassan Dikko ya bayyana Barista Hamza Bala a matsayin halastaccen dan takara maimakon Muhammad Haruna Idris da aka sanar ya lashe zaben
  • Dikko ya ce kotu ta gamsu cewa an take wasu deleget yayin zaben fidda gwanin don haka kuri'unsu na Bala ne

Jigawa - Babbar kotun tarayya da ke zama a Dutse, babban birnin jihar Jigawa ta soke zaben Muhammad Haruna Idris wanda aka ayyana ya lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar APC na dan majalisa mai wakiltan mazabar Kazaure a majalisar jiha.

Da yake zartar da hukuncinsa, alkalin kotun, Justis Hassan Dikko, ya ce kotun ta gamsu ce Muhammad Haruna bai cike ka'idojin shiga takarar zaben ba duba ga takardun makaranta da ya gabatar, Nigerian Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jerin Bukatu 7 Da CAN Ta Gabatarwa Tinubu: Bukatu 2 Da Zai Yiwa Tinubu Wahalan Biya

Tutar APC
Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwani, Ta Bayyana Halastaccen Dan Takarar APC a Jigawa Hoto: Nigerian Tribune
Asali: UGC

Mai shari'a ya ce:

"Hakazalika kotun ta gamsu cewa an takewa wasu daga cikin delegete din yancinsu a yayin zaben fidda gwanin kuma wadannan kuri'un mallakin daya dan takarar ne, Barista Bala Hamza Gada.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Duba ga haka, kotun ta soke zaben Muhammad Haruna Idris sannan ta ayyana daya dan takarar Barista Hamza Gada a matsayin wanda ya lashe zabe."

Saura a sanar da APC da INEC suyi abun da ya dace, lauyan mai kara

Da yake martani, lauyan mai kara, Barista Ibrahim Sa'ad ya nuna gamsuwarsa da hukuncin sannan ya bayyana shi a matsayin nasara ga shari'a da damokradiyya.

Ya bayyana cewa mataki na gaba da za su dauka shine sanar da INEC da APC kasancewarsu cikin shari'ar da kuma neman su bi hukuncin kotu ta hanyar saka sunan Barista Bala Hamza a kan takarda zabe.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa Na Zabi Shettima Musulmi Dan Uwana, Tinubu Ya Yiwa CAN Bayani

Hakazalika a martaninsa, Barista Bala Hamza wanda shine dan majalisa da ke wakiltan mazabar mai ci a yanzu ya ce hukuncin nasara ne ga tsarin shari'a.

Hamza ta kuma yi kira ga abokin adawarsa da ya fito su hada hannu don nasarar APC a dukkan matakai, rahoton Premium Times.

Yan arewa 17 ne ke shugabancin hukumomin tsaro, Atiku

A wani labari na daban, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya dauki alkawarin yin adalci wajen nada shugabannin tsaro idan ya hau kujerar mulki.

Atiku ya zargi gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da nada yan arewa don shugabancin hukumomin tsaro 17 na kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel