Tinubu Ya Tona Masu Lallaban Shi Wajen Samun Takarar Mataimakin Shugaban Kasa
- Asiwaju Bola Tinubu ya yi karin bayani a kan zabinsa na ‘dan takaran mataimakin shugaban kasa
- ‘Dan takaran na jam’iyyar APC yace a cikin masu sukarsa, akwai wadanda suka roki ya ba su tikitin 2023
- Tinubu ya fadawa kungiyar CAN su ajiye maganar addini a gefe, ya ba su misali da Cif Olusegun Obasanjo
Abuja - Asiwaju Bola Tinubu mai neman zama shugaban Najeriya a karkashin jam’iyyar APC mai mulki ya zauna da shugabannin kungiyar CAN.
Punch tace Asiwaju Bola Tinubu ya yi zama na musamman a Abuja tare da Archbishop Daniel Ukoh wanda ke jagorantar kiristocin kasar nan.
Hakan ya zama dole ne a sakamakon sukar ‘dan takaran da kiristoci suke yi saboda ya dauko musulmi irinsa a matsayin mataimakinsa a zabe mai zuwa.
Bola Tinubu ya wanke kan shi daga tuhuma, yana karawa da cewa wasu daga cikin masu sukarsa, sun nemi ya dauke su a matsayin abokan takararsa.
A cewar tsohon Gwamnan na jihar Legas, kai-tsaye ya yi fatali da masu neman takarar mataimakin shugaban kasa, duk da ya bayyana abokansa ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Na sha suka sosai - Tinubu
“Mutane sun soki matakin da na dauka da zafi sosai (na ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa).
Saboda abokai na ne, sun lallabe ni, suna son zama abokan takara, kuma kiri-kiri na ki amincewa da su.”
- Bola Tinubu
Har ya kammala jawabi, ‘dan takaran shugabancin kasar bai ambaci wadannan abokai da yace sun kwallafa rai a zama mataimakin shugaban kasa ba.
Rahoton yace babban ‘dan siyasar ya roki jagororin kiristocin Najeriya su mara masa baya wajen ganin ya samu mulki domin a kawo gyara a kasar nan.
Tikiti: Ba a nan take ba - Tinubu
Tinubu ya tunawa shugabannin kungiyar CAN yadda Olusegun Obasanjo da Atiku Abubakar suka rika rigima da junansu a lokacin da suka yi shugabanci.
Har ila yau, Tinubu ya bada misali da yadda Obasanjo ya kawo masa cikas wajen samar da wuta a yankinsa, duk da shi ma Bayarabe ne ‘danuwansa.
A cewarsa, babu mamaki wata rana a tsaida kiristoci biyu a matsayin ‘dan takaran shugaban kasa da kuma mataimakin shugaban kasa a zaben Najeriya.
Mutuwar 'Dan majalisa a Jos
Kun ji labari Hon. Sobur Olawale ya buga wasan kwallon kafa a bikin cikar Rt. Hon. Mudashiru Obasa shekaru 50, jim kadan kafin ya yi sallama da Duniya.
‘Dan majalisar wanda aka fi sani da Omititi yana tsakiyar shirye-shiryen bikin ‘diyarsa watan nan, kwatsam mutuwa ta fado masa yi wa APC kamfe.
Asali: Legit.ng