2023: Dalilin Da Yasa Na Zabi Shettima a Matsayin Abokin Takarana, Tinubu Ya Magantu Bayan Ganawa Da CAN
- Asiwaju Bola Tinubu ya bayyana ainahin dalilinsa na zabar tsohon gwamnan jihar Borno a matsayin abokin takararsa
- Gabannin zaben 2023, Tinubu ya jaddada cewa bai zabi Kashim Shettima saboda dalili na addini ba illa hakan wata dabara ce
- Dan takarar shugaban kasar na APC ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, bayan ganawa da shugabannin kungiyar CAN
Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Bola Tinubu, ya yi bayanin dalilinsa na zabar tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa a zaben 2023 mai zuwa.
Tinubu wanda ya gana da shugabannin kungiyar kiristocin Najeriya a Abuja a ranar Laraba, ya ce zabar Shettima da yayi dabara ce ba wai addini ba, jaridar The Nation ta rahoto.
Da bayani ga shagabancin CAN, Tinubu ya ce:
“Zabar abokin takarar Kirista da shine abun da zai fi komai sauki amma ba a nan gizo yake saka ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Zabar Shettima da nayi ya samo asali ne daga bukatar gaggauta magance matsalolin da kasar nan ke fuskanta kuma Shettima yana da kwarewa sosai wajen shugabanci wanda ya nuna a lokacin da yake a matsayin gwamnan jihar Borno. Ina son gwamnati mai tarin nasara ne wannan ne dalilin da yasa na zabi Shettima.
“Muna da kalubale na gaggawa wanda baya da nasaba da addini illa a hannayen kwarai wadanda za su iya magance su.”
Tinubu ya daukarwa kungiyar CAN sabon alkawari
Tinubu, wanda ya halarci taron tare da uwargidarsa, Remi, ya ba shugabannin kungiyar tabbacin cewa tikitin Musulmi da Musulmi na APC ba zai zama matsala ba, rahoton Punch.
Dan takarar shugaban kasar ya kara da cewar zai maimaita irin abun da ya yiwa Lagas a matakin tarayya ta hanyar aiki don ra’ayin kowa.
Zaben 2023: Tinubu Ya Nuna Bajintarsa Ta Rawar Da Ba A Saba Gani Ba Yayin Da APC Ta Kaddamar Da Kamfen A Filato
Ya ce:
“Ina neman zama shugaban kasar Najeriya ne ba a kan tafarkin addini ba illa kan kundin tsarin mulki. Godiya ga kungiyar kan gayyatar yan takara domin su yi jawabi kan tsanade-tanaden da suka yiwa kasar.
"Na yarda da bukatar gwamnati mai zaman kanta da kuma bukatar muyi aiki don ra'ayin kasar kamar yadda nayi a jihar Lagas. Na hada kai da Kiristoci don inganta rayuwa da ilimi. Na mayar da makarantun Mishan ga ainahin masu shi wadanda yawancinsu kiristoci ne."
Taron ya kuma samu halartan abokin takarar Tinubu, Kashim Shettima, kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila; mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Boroffice Ajayi, shugaban masu tsawatarwa a majalisa, Orji Kalu da sauransu.
Asali: Legit.ng