Wike Ya Nemi Afuwar Oshiomhole, Ya Nuna Dana Sanin Taimaka Wa Obaseki
- Gwamnan jihar Ribas ya nemi afuwar tsohon shugaban APC, Adams Oshiomhole, bisa abinda ya faru a Edo a watan Satumba, 2020
- A wurin kaddamar da katafariyar gada, Wike yace ya yi nadamar goyon bayan tazarcen gwamna Godwin Obaseki
- Adams Oshiomhole ya je jihar Ribas ne domin amsa gayyatar Wike na bude gadar da ya gina a yankin Obio-Akpor
Rivers - Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya nemi afuwar tsohon shugaban APC na ƙasa, Adams Oshiomhole, yace ya yi dana sanin goyon bayan tazarcen Gwamna Godwin Obaseki na Edo a watan Satumba, 2020.
Wike ya nemi afuwar Oshiomhole ne a wurin kaddamar katafariyar gadar sama a ƙaramar hukumar Obio-Akpor wanda tsohon shugaban APCn ya jagoranta, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Channels tv ta rahoto gwamnan na cewa ya koyi darasi kuma abun da ya riga ya wuce a mance da shi kawai. A kalamansa yace:
"Zan yi amfani da wannan damar na nemi afuwarka. Na je jihar Edo ne domin tabbatar da ɗan takarar da kake so bai kai labari ba. Na ce baza kai nasara ba kuma hakan aka yi."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Na cimma nasarar aikin da aka tura ni a lokacin amma a yanzun an yi walƙiya mun ga fuskar kowa."
Yanzu mun zama abokai, ka yafe mun - Wike
"Yanzun mun zama abokai, abinda ya wuce ya riga ya wuce," inji Gwamna Wike, babban jigo a jam'iyyar PDP ya faɗa wa tsohon shugaban APC na ƙasa.
"Ina mai baka hakuri daga cikin zuciyata. Mutane zasu yabeka idan ka musu abin alheri amma zaka ji maganganu ta ko ina idan kace musu sun yi kuskure."
"Na tabbata mutanen jam'iyyata ba zasu iya komai ba sai da Wike a can baya amma yanzu saboda nace a gyara, a cika alƙawarin da aka ɗauka, to na zama maƙiyi. Su ne fa mutanen da basu da aiki sai yabona dare da rana."
Rikicin PDP: Tsohon Shugaban APC Ya Dira Patakwal Yayin da Wike Ya Cigaba da Ɗasawa da Jiga-Jigan APC
A wani labarin kuma Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa zai goyi bayan ɗan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu a zaben 2023
Da yake jawabi a wurin taron kaddamar da kamfen APC, shugaban ƙasan yace zai haɗa kai da mambobin APC wajen yi wa Tinubu aiki da tallata shi ga yan Najeriya.
A ranar Talata data gabata ne, tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, ya fara gangamin kamfen ɗinsa a Jos, babban birnin jihar Filato.
Asali: Legit.ng