Shugaba Buhari Ya Sha Alwashin Taimaka Wa Tinubu Ya Lashe Zaben 2023

Shugaba Buhari Ya Sha Alwashin Taimaka Wa Tinubu Ya Lashe Zaben 2023

  • Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, yace zai yi wa Bola Tinubu aiki ya zama shugaban ƙasa a 2023 tunda matsayar APC kenan
  • A takaitaccen jawabinsa na wurin kaddamar kamfen APC a Jos, Buhari yace ya zo ne ya miƙa wa ɗan takara tutar jam'iyya
  • Sanata Abdullahi Adamu, ya yaba wa shugaban kasa bisa namijin kokarin da ya yi a mulkinsa musamman a ɓangaren ayyukan raya kasa

Jos, Plateau - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yace zai haɗa kai da mambobin jam'iyyar APC wajen taimaka wa Bola Tinubu ya zama magajinsa a zaɓen 2023.

Buhari ya bayyana haka ne a taƙaitaccen jawabin da ya yi a wurin kaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar APC wanda ya gudana ranar Talata a Jos, jihar Filato.

Wurin taron APC a Jos.
Shugaba Buhari Ya Sha Alwashin Taimaka Wa Tinubu Ya Lashe Zaben 2023 Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Facebook

A rahoton Premium Times, Shugaban ƙasa ya ce:

Kara karanta wannan

Kamfen 2023: Bidiyon Yadda Harshen Bola Tinubu Ya Kucce, Yace Allah Ya Albarkaci PD....APC

"Jam'iyya ta ɗauki matsaya saboda haka zamu goya masa baya kuma mu tallata takararsa domin 'yan Najeriya su kaɗa masa kuri'u ya zama shugaban Najeriya."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ba zan yi dogon jawabi ba, na zo nan ne domin na miƙa masa tutar jam'iyyarmu."

Zuwanka karramawa ce a gare mu - Adamu

Da yake nasa jawabi, shugaban APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, yace jam'iyyar ta taki sa'a da ta samu halartar mai girma shugaban ƙasa a wurin Ralin yakin neman zaɓenta.

Adamu, yace zuwan shugaba Buhari ya nuna cewa zuciyarsa na tare da jam'iyya da baki ɗaya 'yan takararta.

Ya kuma bayyana cewa nasarorin da shugaba Buhari ya samu a ɓangaren manyan ayyukan raya ƙasa sun kere na shugabannin da suka gabace shi.

Adamu yace:

"Ina rokonku da ku miƙe tsaye ku tafa wa shugaban ƙasa saboda ƙwazonsa. Jam'iyyarmu ta yi abin azo a gani, mun yi alƙawarin kawo canji kuma an samu canji."

Kara karanta wannan

Tinubu: Zan Kora Wani Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Koma Mahaifarsa a 2023, Ya Faɗi Suna

Adamu ya kara da cewa miƙa wa ɗan takara tutar jam'iyya alama ce da ke nuna iznin ya jagoranci jam'iyyar APC a babban zaɓen 2023 mai zuwa.

A wani labarin an hangi manyan jaruman Fim daga masana'antun Kannywood da Nollywood a wurin kamfen Bola Tinubu a Jos, jihar Filato

Jarumi Ali Nuhu na daga cikin waɗanda suka ƙara ƙayata wurin daga Kannywood kuma sun ba da nishaɗi a wakoki daban-daban.

Sarki Ali yace shi da takwarorinsa abokan sana'arsa zasu yi aiki tukuru domin ganin mutane sun amince su zaɓe Bola Tinubu a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262