Duk Wanda Ya Ci Zabe Shi Zan Mika Wa Mulki a 2023, Inji Buhari a Filin Gangamin Tinubu
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake nanata matsayarsa a ranar Talata 15 ga watan Nuwamba cewa, zaben 2023 za a yi shi cikin adalci da gaskiya
- Ya bayyana hakan ne a filin wasa na Gbong Gwom a birnin Jos, inda yace babu dan takarar da zai ci zabe a tauye masa hakkinsa
- Duk da haka, Buhari ya bayyana goyon bayansa ga tafiyar Bola Tinubu da Kashim Shettima a zaben mai zuwa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce, zai tabbatar duk wanda ya lashe zaben 2023 daga kowace jam'iyya ce ya samu 'yancin hawa kujerar shugaban kasa.
Buhari ya ce, babu dan takarar da zai lashe zabe kana a tauye masa hakkinsa saboda wani dalili.
Ya bayyana hakan ne a ranar Talata 15 ga watan Nuwamba a filin wasa na Gbong Gwom yayin kaddamar da kamfen na jam'iyyar APC.
A cikin wata sanarwa da hadiminsa Garba Shehu ya fitar, Buhari ya nanata akidarsa ta tabbatar da an yi zabe cikin lumana da gaskiya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewar Buhari:
"Babu wanda zai ci zabe sannan a hana shi hakkinsa, ba tare da la'akari da jam'iyyar da suka fito ba."
Dalilin da yasa Buhari ya yi tsokaci
A cewar Garba Shehu, maganar Buhari martani ce ga abin da daraktan kamfen APC, gwamna Simon Lalong ya fada a filin taron.
Lalong ya ce, APC za ta maimaita tarihin abin da ya faru shekaru 30 da suka shude, lokacin da dan takarar SDP, Moshood Abiola ya lashe zaben shugaban kasa.
Buhari ya ce:
"Wancan nasaran zaben da aka yi sojoji sun lalata shi."
Dalilin da yasa aka zabi Jos don kaddamar kamfen APC
A wani labarin, gwamna Lalong na jihar Filato ya fadi dalilin da yasa jam'yyar APC ta zabi fara kamfen dinta a birnin Jos, kuma a Arewacin Najeriya.
A cewarsa, a jihar Filato ne MKO Abiola ya fara gangami, a nan kuma ya ci zaben 1993 da aka gudanar shekaru 30 da suka gabata.
A cewarsa, tarihi zai maimaita kansa, domin Tinubu dan yankin su Abiola ne, kuma tabbas zai lashe zaben 2023 mai zuwa tare da yaikinin tafiyar da lamuran kasar nan.
Asali: Legit.ng