Peter Obi Ne Mafi Cancantan Dan Takara, Inji Dan Gwamna Soludo da Ya Saba da Ra'ayin Mahaifinsa
- A makon nan ne gwamnan jihar Anambra, farfesa Chukwuma Soludo ya nuna baya goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi
- Gwamnan ya rubuta doguwar takardar da ya bayyana matsayarsa da cewa, Peter Obi ba zai yi nasara ba a zaben 2023
- Maganar Soludo dai ta jawo cece-kuce, inda dansa, Ozinna ya bayyana ra'ayin mai bambanci da mahaifinsa
Facebook - Ozonna Soludo, dan gwamnan jihar Anambra ya bayyana ra'ayinsa kan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour a zaben 2023 mai zuwa.
Matashin mai shekaru 28 da ke zaune a Burtaniya ya yi tsokaci a shafin Facebook kan wani rubutu da ke caccakar mahaifinsa da ya ce Peter Obi ba zai ci zabe a 2023 ba.
A ranar Litinin 14 ga watan Nuwamba, Farfesa Soludo ya ce sam Peter Obi ya san ba zai ci zabe ba, kawai dai yana takara ne a zaben mai zuwa.
Gwamnan na Anambra ya kuma yi zargin cewa, talauci da fatara karuwa suka yi a Anambra a lokacin mulkin Obi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan a mutun Obi sun caccaki Soludo
Wannan lamari dai ya haifar da cece-kuce a shafin sada zumunta, mutane da dama 'yan a mutun Obi sun caccaki gwamnan na Anambra.
Yayin da ake ta kokarin jawo dan Soludo, Ozonna cikin lamarin, shi kuwa ya fito ya bayyana ra'ayinsa sabanin na mahaifinsa.
A kalamansa:
"Zan zo ba a tsoma ni cikin wannan ba. Ni ba na kan ra'ayin kowa. Ina da nawa ra'ayin kuma a kullum ina tunanin Peter Obi ne dan takara mafi cancanta. Duk wannan bani da alaka dashi."
'Obidients' sun fusata bayan da Soludo ya yiwa Obi tonon silili
A tun farko kun ji cewa, gwamna Soludo ya yiwa Peter Obi tonon silili kan kasuwancin da ake cewa ya habaka a jihar Anambra lokacin da yake gwamna.
Soludo ya fito a gidan talabijin ne, inda ya yi kaca-kaca da jarin kasuwancin da ake cewa Obi ya gina a jiharsa.
Maganganun da Soludo ya yi sun fusata 'yan a mutun Obi, inda suka yi ta maganganu masu zafi kan gwamnan mai ci na Anambra.
Asali: Legit.ng