Kotun Daukaka Kara Ta Fatattaki Akpabio Matsayin ‘Dan Takarar Sanata

Kotun Daukaka Kara Ta Fatattaki Akpabio Matsayin ‘Dan Takarar Sanata

  • Kotun daukaka kara dake babban birnin tarayya na Abuja ta fatattaki Sanata Godswill Akpabio matsayin ‘dan takarar sanatan Akwa Ibom ta arewa maso yamma
  • A hukuncin da kwamitin alkalai uku wanda ya samu jagorancin Jastis Danlami Senchi ya zartar, Akpabio bai kawo shaidu ba a kan lokaci
  • Hakazalika, hukuncin ya bayyana cewa matsayinsa na ‘dan takarar shugaban kasa, bai shiga zaben fidda gwani da INEC ta lura da shi ba na ranar 28 ga Mayu

FCT, Abuja - Kotun daukaka kara dake Abuja ta fatattaki Sanata Godswill Akpabio matsayin ‘dan takarar kujerar sanatan Akwa Ibom ta arewa maso yamma a karkashin jam’iyyar APC, Channels TV ta rahoto.

Sanata Godswill Akpabio
Da Duminsa: Kotun Daukaka Kara Ta Fatattaki Akpabio Matsayin ‘Dan Takarar Sanata. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC

A yayin yanke hukunci, kwamitin alkalai uku da suka samu jagorancin Mai shari’a Danlami Senchi, ya yanke hukuncin cewa Akpabio ya gaza bayyana shaidun shari’ar a kan lokaci kamar yadda tanadin shari’a ya bayyana, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna Kwankwaso Ya Fallasa Asirin Gwamnoni na Satar Dukiyar Talakawa

Akpabio bashi da damar shiga zaben fidda gwanin 28 ga Mayu

Kwamitin ya kara da yanke hukuncin cewa, Akpabio matsayin ‘dan takarar kujerar shugabancin kasa a APC bashi da damar shiga zaben fidda gwani na ranar 28 ga watan Mayu kuma wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta lura da shi, wanda ya samar da Udom Ekpoudom matsayin ‘dan takara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kotun daukaka karar ta soke hukuncin babbar kotun tarayya dake Abuja wanda a ranar 22 ga watan Satumba ya bukaci INEC da ta ayyana Sanata Akpabio matsayin ‘dan takarar sanatan APC wanda ya ci zaben fidda gwani karo na biyu wanda aka yi a ranar 9 ga watan Yuni.

Irin Makomar Akpabio ce ta Sanata Ahmad Lawan

Irin wannan abunda ya faru da Sanata Godswill Akpabio ne ke faruwa da Sanata Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawa Najeriya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: APC Ba Tada Dan Takarar Gwamna A Akwa Ibom, Kotu Tace A Sake Zabe

Lawan da Akpabio duk sun nemi kujerar shugabancin kasa inda aka lallasa su a zaben fidda gwanin da aka yi wanda ya samar da Tinubu matsayin ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC.

Sai dai daga Lawan har Akpabio sun koma mazabunsu inda suka sake neman komawa a tsayar dasu ‘yan takarar sanatoci.

Hakan kuwa bai yuwu ba saboda wadanda suka yi nasarar samun tikitin takarar sun dire gefe tare da cewa ba zasu hakura ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng