Hukumar NBC Ta Ci Tarar Gidan Talabijin Na Arise Bisa Yada Labaran Karya Akan Tinubu
- Akalla kwanaki biyu bayan yada labarin da ke da'awar hukumar zabe na bincike kan yiwuwar harkallar Tinubu ta miyagun kwaya, an ci tarar gidan talabijin na Arise
- Hukumar yada labarai ta kasa ne ta bayyana cin tarar gidan talabijin din har N2m bisa saba doka da ka'idar yada labarai a Najeriya
- A baya kadan, gidan talabijin din ya nemi afuwar Tinubu bisa yada labarin bai da tushe balle makama, kamar yadda rahotanni suka kawo
FCT, Abuja - Hukumar yada labarai ta kasa (NBC), ta ci tarar gidan na Arise bisa yada rahotannin karya kan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu.
An ci tarar gidan talabijin din N2m bisa laifin saba ka'idar yada labarai na hukumar, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
A ranar Lahadin da ta gabata, Arise Tv ta nemi afuwa bayan yada rahoton cewa, hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) na binciken Tinubu kan zargin harkallar miyagun kwayoyi da ke da asali a kasar Amurka.
INEC a karshen makon jiya ta karyata rahoton Arise Tv tare da yin karin bayani a kai, rahoton Vanguard.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Arise Tv ya nemi afuwar Bola Tinubu
Wannan lamari dai ya sa gidan talabijin din ya gaggauta sauke labarin tare da neman afuwa daga dan takarar na APC.
Takardar cin tarar na dauke da sa hannun Dele Adeleke, mai ba da shawari na musamman kan harkokin yada labarai na babban daraktan NBC, Balarabe Shehu Ilelah.
Dele ya bayyana cewa, rahoton na Arise tuni ya fara jawo matsala a kasar, don haka akwai bukatar hukunta gidan talabijin din don gaba.
Tuni kafafen sada zumunta suka dauki zafi tun bayan yada labarin yiwuwar Tinubu na da hannu a harkallar miyagun kwayoyi.
Jigon PDP ya caccaki Tinubu da Peter Obi
Bayan samun labarin alakar Tinubu da miyagun kwayoyi, jigon PDP ya caccaki dan takarar shugaban kasan na jam'iyyar APC mai ci.
Ya ce, idan aka kwatanta dan takarar shugaban kasan PDP, Atiku Abubakar da Tinubu, to tabbas za a samu Atiku a matsayin waliyyi.
Hakazalika, ya duba batun Peter Obi na jam'iyyar Labour, inda ya ce shi kuma ya kasance ana masa zargin rashawa a takardun Pandora.
Asali: Legit.ng