Yadda Najeriya Tayi Mani Riga da Wando, Rabiu Kwankwaso Yace Ya Taki Sa’a a Siyasa
- Rabiu Musa Kwankwaso ya zanta da jama’a a game da batun neman takaran da yake yi a zaben 2023
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana neman mulkin Najeriya a karkashin jam’iyyar adawa ta NNPP
- ‘Dan takaran yace yana cikin ‘yan siyasar suka fi kowa takar sa’ar samun damar yi wa jama’a hidima
Abuja - Rabiu Musa Kwankwaso yana ganin cewa siyasa tayi masa gata da rana a Najeriya, ganin irin mukamai da matsayin da ya rike a tarihi.
Rabiu Musa Kwankwaso mai harin kujerar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP a 2023, ya zanta da gidan talabijin Channels TV a kan batun takararsa.
Da yake jawabi a ranar Lahadi, 13 ga watan Nuwamba 2022, Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa yana cikin wadanda suka fi kowa sa’a a siyasa.
‘Dan siyasar yace ya samu damammaki iri-iri da ya yi amfani da su wajen yi wa al’umma hidima.
Mukamai iri-iri a shekaru 30
A wani bidiyo da Legit.ng Hausa ta saurara, an ji Kwankwaso yana jero irin mukamai da manyan kujerun siyasa da ya rike a cikin shekaru 30.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Dan takaran shugaban kasar ya bada labarin shigarsa siyasa a 1992 da yadda ya yi kokari ha rya zama mataimakin shugaban majalisar wakilai.
Bayan sojoji sun hambarar da gwamnati ya bar majalisar tarayya, Kwankwaso yace sun yi ta kafa kungiyoyin siyasa da shirin komawa mulki.
Bayan haka, fitaccen ‘dan siyasar yace ya lashe zabe a karamar hukumar Madobi domin zuwa taron kasa inda aka shirya kundin tsarin mulkin 1999.
A cewarsa, sun bi Janar Shehu Musa ‘Yaradua (rtd) har zuwa lokacin da shi ya zama jagoran jam’iyyar DPN a jihar Kano bayan rasuwar Marigayin.
Kafa tarihi bayan fadi zaben Kano
Tsohon Sanatan yake cewa sannu a hankali ya zama Gwamnan jihar Kano a 1999, amma ya rasa zaben tazarce, wanda hakan ya sa ya zama Minista.
A wannan bidiyo, za a ji ‘dan siyasar yana bada labarin yadda ya rungumi kaddara a 2003, ya taya wanda ya yi nasara murnar zama Gwamnan Kano.
Har zuwa nan gaba, Kwankwaso yace yana sa ran cigaba da samun irin wannan sa’a a fagen siyasa.
Asali: Legit.ng