2023: Dubbannin Mambobin Jam'iyyar APC da LP Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Arewa

2023: Dubbannin Mambobin Jam'iyyar APC da LP Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Arewa

  • Jam'iyyar PDP mai mulkin jihar Taraba ta kama hanyar murkushe adawa a shiyyar Sanatan Kudancin jihar gabanin 2023
  • A ranar Asabar da ta gabata, dubbanin mambobin APC, LP da wasu jam'iyyu suka sauya sheka zuwa PDP Laima
  • Masu sa ido da sharhi a siyasar jihar sun ce duk da haka jam'iyyun adawa ka iya ba PDP mamaki idan bata tashi tsaye ba

Taraba - Karshen makon nan bai zo wa jam'iyyar APC da LP da kyau ba a jihar Taraba, arewa maso gabashin Najeriya, sakamakon rashin dubbanin magoya bayansu.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa dubbannin mambobin jam'iyyun APC da LP ne suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP mai mulkin jihar a shiyyar Sanatan Kudancin Taraba.

Magoya bayan PDP.
2023: Dubbannin Mambobin Jam'iyyar APC da LP Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Arewa Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Rahotanni sun tabbatar da cewa guguwar sauya sheƙar bata tsaya iya nan ba, ta shiga har wasu jam'iyyu na daban a yankunan ƙananan hukumomi 5 da suka haɗa shiyyar.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Da Tinubu Sun Rasa Wasu Magoya Bayansu a Wata Jihar Arewa, Sun Koma Jam’iyyar Kwankwaso

Danɗazon 'yan siyasan sun yi tururuwa a wurin kaddamar da kamfen takarar Sanata na gwamnan jihar mai ci, Darius Ishaku ranar Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan takarar gwamnan Taraba a inuwar PDP, Kefas Agbu, da takwaransa na jam'iyyar LP, Joel Ikenya, duk haifaffun ƙaramar hukuma Wukari ne a shiyyar kudancin jihar.

Tsohon mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar Dattawa, Emmanuel Bwacha, wanda yanzu haka ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin Kotun Jalingo da ta soke sahihancin takararsa a APC, ya hito ne daga Donga duk a kudu.

Yayin da ake dakon martanin da jam'iyyun adawa ka iya yi game da batun guguwar canza sheka dake cin ganiyarta a shiyyar, masu sa ido a siyasa sun yi hasashen karin sauya sheka nan da 'yan makonni idan Kamfe ya kankama.

Haka zalika masu sharhi a siyasar jihar na fatan jam'iyyun adawa su ba PDP wahala matuƙar jam'iyyar bata tashi tsare wurin jawo hankalin masu kaɗa kuri'a tun daga tushe ba kafin zuwan zaɓe.

Kara karanta wannan

2023: Kada Yan Najeriya Su Cire Rai, APC Zata Kawo Canjin da Suke Bukata, Tinubu

APC na yi nasarar lashe zaben kananan hukumomin jihar Neja

A wani labarin kuma jam'iyyar mai mulkin jihar Neja ta lashe zaɓen kananan hukumomin jihar Neja baki ɗaya

Hukumar zaɓen jihar mai zaman kanta (NSIEC) tace zaɓen da aka gudanar ranar 10 ga watan Nuwamba, 2022 ya kammala cikin zaman lafiya.

Duk da jam'iyyar PDP ba ta shiga zaɓen ba yayin da ta kai ƙara Kotu, hukumar tace jam'iyyu 12 ne suka fafata a kujerun Ciyamomi da Kansiloli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262