2023: APC Da PDP Sun Rasa Wasu Mabiyansu a Jihar Gombe, Sun Koma Jam’iyyar NNPP
- Jam’iyyar NNPP ta Kwankwaso ta kara samun karfi a jihar Gombe a ranar Lahadi yayin da mambobin APC da PDP suka dawo cikinta
- Masu sauya shekar sun samu tarba daga dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP a jihar, Khamisu Mailantarki
- Wannan karin karfi ne ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar kuma tsohon gwamnan jihar Kano
Gombe - Wasu mamabobin jam’iyyun All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) sun sauya sheka zuwa jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a karamar hukumar Kaltungo da ke jihar Gombe.
Da yake tarban masu sauya shekar, dan takarar gwamna na NNPP a jihar, Khanmisu Mailantarki, da sauran jiga-jigan jam’iyyar sun taya sabbin mambobin murnar samun mafaka a jam’iyyar, jaridar Punch ta rahoto.

Source: Twitter
A cewar Mailantarki, dawowar jam’iyyar a wannan lokaci babban nasara ne, yayin da ya basu tabbacin cewa za su kasance a duk wasu harkoki na siyasarsa.
Ya ce daga PDP har APC sun samu damar mulkar jihar a shekarun baya, sai dai ya yi zargin cewa basu tabuka komai ba kamar yadda al’ummar jihar suka yi tsammani.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Mailantarki ya bayyana cewa NNPP za ta samar da mafita da ake bukata a shekara mai zuwarahoton Blueprint.
Daga karshe ya bukaci sabbin masu sauya shekar da su tattaro mutane a wurarensu.
Dan takarar gwamnan ya ce:
“Godiya ta tabbata ga Allah kan wannan nasara da NNPP ke samu a kullun kwanan duniya. Wannan sakamakon manufofi masu inganci da jam’iyyar ta tanadar ne. wannan ne dalilin da yasa Karin mutane masu yawan gaske ke tururuwan shigowa. A tare, za mu iya sannan mu samu sabuwar jihar Gombe a 2023.”
Yakamata APC ta takawa Shettima burki game da kalamansa a kan yan takarar shugaban kasa, jam'iyyar LP
A gefe guda, Legit.ng ta kawo a baya cewa jam'iyyar Labour Party ta kalubanci abokiyar adawarta ta APC a kan ta gargadi dan takararta da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.

Kara karanta wannan
Zaben 2023: Jam'iyyar APC Na Rasa Ƙarfinta A Kudu Maso Kudu Yayin Da Ɗaruruwan Mambobinta Suka Koma PDP A Babban Jiha
Jam'iyyar LP ta zargi Shettima da yin kalaman tozarci ga dan takararta na shugaban kasa, Peter Obi da sauran masu neman takarar kujera ta daya a kasar.
Asali: Legit.ng
