2023: Duk Talaucin Gidanku, PDP Zata Baku Damar Cimma Muradanku, Atiku Ga Matasa
- Dan takarar shugaban kasa na PDP ya daukarwa matasa gagarumin alkawari idan har ya gaje Buhari a 2023
- Atiku Abubakar ya yi hasashen cewa za a yi waje da jam'iyya mulki a kasar a babban zabe mai zuwa
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi alkawarin inganta rayuwar matasa idan ya lashe zabe mai zuwa
Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya ce idan aka zabe shi, gwamnatinsa zata budewa matasa hanyoyin samu.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a wajen ratsar da reshen matasa na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP a Abuja, TheCable ta rahoto.
APC zata zama tarihi bayan 2023
Atiku ya ce za a yi waje da jam'iyyar APC a zaben 2023 saboda sun dakushe duk wasu burika na yan Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Punch ta rahoto cewa Atiku wanda ya bayyana APC a matsayin kungiyar hadin gwiwa ba wai jam'iyya ba, ya ce a iya saninsa, PDP kadai ce jam'iyya a Najeriya.
Ya ce ya taka muhimmiyar rawar gani wajen yaki don tabbatar da dorewar damokradiyar Najeriya, yana mai cewa wannan ne dalilin da yasa matasa ke shan romon yanci a yau.
Ya ce:
"Magana ta gaskiya, PDP ce jam'iyyar siyasa daya tilo. APC ba jam'iyyar siyasa bace; gamayar CPC da jam'iyyar Tinubu ce. Kungiyar hadin gwiwa ce. Kuma mun ga cewa duk jam'iyyun hadin gwiwa a kasar nan sun bace bat.
"Bari na fada maku; duk talaucin gidanku, PDP zata baku damar zama abun da kuke son zama a Najeriya."
Na fahimci duk matsalolin Najeriya - Atiku
Atiku ya ce ya fahimci matsalolin kasar kuma ya tsara wasu ajanda guda biyar don ci gaban kasar.
Ya kara da cewa:
"Kun san dalilina na fadin haka? Saboda wadannan ajanda biyar, da kaina na zauna na rubuta su. Ban tambayi kowani Farfesa ba.
"Idan ka yi nazari kan wadannan manufofi biyar - daga hadin kan kasa, tsaro, ilimi zuwa sauya fasalin lamura - za ku gano cewa suna da alaka.
"Don haka, ina mai baku tabbaci. Duk talaucin gidanku, duk matsayinku, PDP zata taimaka wajen ganin kun cimma burikanku a kasar nan.
"APC ta zo sannan ta dakushe muradan yan Najeriya. Bama sa ran zasu kawo chanji ta kowani bangare a cikin watanni biyar zuwa shida masu zuwa."
Abubakar ya shawarci matasa da su bi duk lungu da sako na kasar don jan hankalin yan Najeriya su zabi PDP.
Najeriya na bukatar shugaban kasa mai fadar gaskiya
Da yake jawabi, Ifeanyi Okowa, gwamnan jihar Delta kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa na PDP, ya ce Najeriya na bukatar shugaba wanda ya fahimci matsalolin kasar kuma wanda zai iya magance su.
Okowa ya kara da cewar Najeriya na bukatar shugaba wanda zai iya fadar gaskiya a kodayaushe, ya riki kundin tsarin mulkin kasar nan sannan ya mutunta duk dokokin da ke kasa.
Asali: Legit.ng