Mataimakin Shugaban Jam'iyya Labour Party Na Kasa Ya Rasu

Mataimakin Shugaban Jam'iyya Labour Party Na Kasa Ya Rasu

  • Allah ya yi wa mataimakin shugaban jam'iyyar LP na shiyyar arewa ta tsakiya, Adi Shirsha Adi, rasuwa yana da shekara 61 a duniya
  • Kakakin jam'iyyar LP ta ƙasa, Olufemi Arabambi, yace Marigayi Adi ya rasu ne bayan fama da gajeriyar rashin lafiya ranar Laraba
  • Jam'iyyar LP ta miƙa ta'aziyyarta ga iyalan marigayin wanda ya fito daga jihar Benuwai

Abuja - Mataimakin shugaban jam'iyyar Labour Party (LP) ta ƙasa na shiyyar arewa ta tsakiya, Kwamaret Adi Shirsha Adi, ya rigamu gidan gaskiya.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Sakataren watsa labarai na jam'iyyar LP ta ƙasa, Olufemi Arabambi, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

Jam'iyyar Labour Party.
Mataimakin Shugaban Jam'iyya Labour Party Na Kasa Ya Rasu Hoto: vanguardngr

Yace Kwamaret Adi ya rasu ne ranar Laraba bayan fama da rashin lafiya ta ɗan lokaci yana da shekaru 61 a duniya.

Kara karanta wannan

Rigimar PDP: Gwamnan Bauchi Ya Magantu Kan Wasikar Fushin da Ya Rubuta da Ganawarsa da Atiku

Sanarwan tace:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Shugaban jam'iyya, Barista Julius Abure, a madadin kwamitin gudanarwa da kwamitin zartaswa na LP ta ƙasa, na mai baƙin cikin sanar da rasuwar mataimakin shugaba (arewa ta tsakiya), Adi Shirsha Adi."
"Ya mutu ne ranar Laraba (9 ga watan Nuwamba, 2022) bayan fama da rashin lafiya ta ɗan lokaci."

Mun kaɗu da jin labarin - LP

Mista Arabambi ya bayyana rasuwar kwamaret Adi a matsayin labarin kaɗuwa, inda yace za'a yi kewar gudummuwarsa wurin kafa gwamnatin da al'umma ke fata.

"Jam'iyya ta shiga jimamin rasuwar Adi Shirsha Adi saboda mutum ne mai sadaukarwa, wanda ya ba da gudummuwa wajen gina LP a shiyyarsa kana ta roki iyalansa su jure wannan rashi."
"Wannan ba irin labarin da muke fatan yaɗa wa bane, amma a matsayin masu Imani, ba zamu ce meyasa Allah ya ɗauke shi ba, ya fi mu sanin daidai. Bamu da zaɓi sai dai mu gode wa Allah."

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Wani Mahaifi Ya Zuba Wa Ɗiyarsa Ta Cikinsa Guba a Shayi Kan Soyayya

Jam'iyyar LP ta roki iyalan mamacin su yi koyi da kyawawan halayen mahaifinsu. Marigayi Adi ya fito ne daga karamar hukumar Konshisha, jihar Benuwai.

A wani labarin Sanata Kashin Shettima Ya Bayyana cewa ɗan takarar LP, Peter Obi ba zai iya tabuka komai ba, haka takwaransa na PDP, Atiku

Ɗan takarar mataimakin shugaban kasa a inuwar APC, Kashim Shettima ya yi ikirarin cewa ko da Obi da Atiku sun ci nasara, ba zasu iya yiwa yan Najeriya abinda suke so ba.

A jawabin da ya yi a wurin wani taro a Abuja, tsohon gwamnan ya nuna kwarin guiwar cewa kwaf ɗaya Tinubu zai wa Atiku da Obi ya zama zaɓaɓɓen shugaban ƙasa a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262