Rigimar PDP: Babban Dalilin Da Ya Hana Shugaban PDP Halartar Kamfen Atiku a Borno

Rigimar PDP: Babban Dalilin Da Ya Hana Shugaban PDP Halartar Kamfen Atiku a Borno

  • Rashin ganin shugaban PDP na ƙasa a wurin gangamin kamfen Atiku Abubakar a Maiduguri ranar Laraba ya ta da kura
  • Babba mai taimaka wa Iyorchia Ayu kan harkokin sadarwa yace wasu muhimman taruka ne suka hana shi zuwa
  • Wannan ba shi ne na farko ba, a ranar Litinin Ayu bai je wurin kaddamar da kwamitin kamfen PDP a jihar da ya fito ba

Abuja - Rashin ganin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, a wurin gangamin yakin neman zaɓen Atiku a Maiduguri, jihar Borno ya tada kura a tsakanin masu ruwa da tsakin jam'iyyar.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa tun kafin rashin ganinsa a taron yau Laraba, Ayu ya kaucewa taron kaddamar da kwamitin yakin neman zaɓen gwamna, 'yan majalisun jiha da na tarayya a Makurdi, jihar Benuwai ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Bayan Ganawa Da Babban Na Hannun Damar Atiku, Wike Ya bayyana Matsayinsa na Karshe Kan Rikicin PDP

Shugaban PDP, Ayu.
Rigimar PDP: Babban Dalilin Da Ya Hana Shugaban PDP Halartar Kamfen Atiku a Borno Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Da yake bayani kan dalilin rashin ganin Ayu a Maiduguri, babba mai taimaka wa shugaban PDP ta fannin midiya da sadarwa, Simon Imobo-Tswam ya ce:

"Wasu muhimman taruka ne suka rike shi ya gaza zuwa, wannan ba abin ɗaga murya bane domin manyan kusoshi sun wakilce shi a wurin bisa jagorancin mataimakin shugaban (arewa)."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ba zato, shugaban PDP na ƙasa ya hito ne daga mazaɓar Santan Benuwai na shiyyar B, yankin da gwamnan jihar Samuel Ortom, ya fito.

Ortom na ɗaya daga cikin gwamnonin jam'iyyar PDP guda 5 da ake kira G5, waɗanda suka tsaya tsayin daka kan dole Ayu ya yi murabus idan ana son zaman lafiya.

Rigingimu kala daban-daban sun hana PDP zaman lafiya tun bayan gama zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa, wanda Atiku ya lallasa Wiike da sauran 'yan takara a watan Mayu.

Kara karanta wannan

2023: Wasu Daga Cikin Gwamnonin Tsagin Wike Na Shirin Yaudararsa, Zasu Koma Bayan Atiku

Tun wannan lokaci Wike da gwamnonin jihohin Abiya, Oyo, Enugu da Benuwai tare da wasu jiga-jigan PDP suka ware kansu, kana suka jaddada cewa ba zasu shiga kamfen takarar shugaban ƙasa ba.

Harin da aka ce yan daba sun kai wa Atiku karya ne - APC

A wani labarin kuma Kalaman kakakin kwamitun kamfen PDP, Dino Melaye na cewa APC ta tura yan daba sun farmaki Ayarin Atiku sun bar baya da ƙura

Jim kaɗan bayan labarin ya karade kafafen sada zumunta, APc ta fito tabƙaryata ikirarin Melaye, tace babu wanda ya farmaki Ayarin PDP a Maiduguri

A wata sanarwa domin martani kan zargin da aka rataya mata, APC tace tun zuwan Zulum aka magance Dabanci a siyasar jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262