Sanatan APC, Adamu Bulkachuwa Ya Sauya Sheka, Ya Kama Tafiyar Atiku
- Jam'iyyar adawa ta PDP na ci gaba da samun karuwa a 'yan kwanakin nan a Arewacin Najeriya gabanin zaben 2023
- A jihar Bauchi, jam'iyyar ta yi babban kamu, domin kuwa wani jigon APC ne ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP
- A wata tattaunawa a Bauchi, gwamna Ortom ya nemi gafarar Fulani da ya kira 'yan ta'adda a kwanakin baya
Jihar Bauchi - Burin Tinubu na gaje kujerar shugaba Buhari a zaben 2023 na ci gaba da gamuwa da tasgaro yayin da a kullum ake samun wadanda ke ayyana sauya sheka zuwa wasu jam'iyyu.
Sauya shekar wasu jiga-jigan APC a kwanakin nan na sake jefa alamar tambaya ga jam'iyyar tare da hango makomarta a zaben 2023 mai zuwa.
A kokarin tafiyar 2023, wasu mambobin APC ba su ji a jikinsu jam'iyyar za ta tabuka wani abu ba, musamman duba da shugabancinta, yayin da wasu kuwa ke duba rikicin da ke cikin jam'iyyar.
Sanata Adamu Bulkachuwa ya sauya sheka zuwa PDP
A wannan karon, sanata mai wakiltar Bauchi ta Arewa, Adamu Bulkachuwa ya bayyana ficewarsa daga APC tare da kama jam'iyyar PDP mai mulkin jihar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wannan na zuwa ne a cikin rahoton da Rivers Mirror ta wallafa a shafinta na Facebook a yau Laraba 9 ga watan Nuwamba tare da hoton lokacin da ake tarbar sanatan.
A hoton da aka yada, an ga lokacin Bulkachuwa ya daga katin shaidar shiga jam'iyyar PDP mai adawa a kasar.
Ba jam'iyyar APC kadai ke cikin rikici ba, ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin dan takarar shugaban kasa na PDP da wasu gwamnonin jam'iyyar da ke adawa da tafiyarsa.
Ortom ya nemi gafarar 'yan Najeriya kan furucin muzanci da ya yiwa Fulani
A wata ziyara da gwamnonin PDP na G-5 suka kai jihar Bauchi a yau, gwamna Ortom ya gana da 'yan jarida, ya tattauna batutuwa da suka shafi tafiyar siyasar kasar nan.
A baya Ortom ya ce ba zai taba goyon bayan Bafulatani ya zama shugaban kasar Najeriya ba, saboda Fulani 'yan ta'adda ne kuma suna kashe 'yan jiharsa.
Sai dai, a yau ya yi amai ya lashe, ya ce bai fadi wadannan kalamai yadda ake yadawa ba, ba fahimce shi bane, kuma ya ba da hakuri.
Asali: Legit.ng