2023: Sabbin Rigingimu Sun Kunno Kai a Jam'iyyar PDP Kan Kuɗin Kamfen Atiku
- Alamu na nuna abubuwa na ci gaba da cakudewa jam'iyyar PDP game da harkokin yakin neman zaɓen Atiku
- Bayanai sun nuna cewa ana ta luguiguita batun karancin kuɗin kamfe, har an fara yaɗa shugaban kwamiti na shirin murabus
- Jam'iyyar PDP da shi kansa shugaban kwamitin kamfe sun musanta rahoton amma da alamu akwai wani abu a ƙasa
Abuja - Duk da har yanzun jam'iyyar PDP ba ta iya shawo kan gwamna Wike da 'yan tawagarsa ba, alamu sun nuna cewa taƙaddama ta sake ɓarke wa a jam'iyyar kan rashin kudin kamfen shugaban kasa.
Punch ta ruwaito cewa bayanan da ke nuna babu isassun kuɗin yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar ka iya zama gaskiya idan har za'a ɗauki wasu kalaman mambobin kwamitin zartaswa na PDP (NEC).
Wani jigon PDP daga yankin kudu maso yamma da ya nemi a ɓoye bayanansa yace ko kaɗan bai yi mamaki ba idan aka ce kuɗin kamfe sun jawo matsala a jam'iyyar.
Yace ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, duk shi za'a dora wa laifin kuma ya cancanci haka.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yace, "Anata ƙorafin Atiki ya matse aljihu ba shi da niyyar sakin kuɗi a tallata takararsa, amma da bakinsa wani Lokaci Atiku ya faɗa wa wasu gwamnoni cewa ya ware Biiliyoyi na kamfe."
"Shiyasa gwamnoni suka rungumi hannu suna kallonsa suka nuna ba zasu ba da gudummuwar ko sisi ba, wasu gwamnonin ma ba su da tabbacin nasara kuma ba su shirya buɗe lalitarsu ba. Watakila a samu canji cikin makonnin nan."
Meyasa Atiki ya ki sakin kudin?
Da yake fatali da jita-jitar ko Aljihun Atiku ya yi ƙasa ne, Jigon ya ƙara da cewa, "Ɗan takarar na shirin sakin kuɗin ne ana gab da karkare kamfe, ya ɗauki darasi daga abinda ya faru a 2019."
"Ya sha kaye a wancan zaɓen, mai yuwuwa yanzu idonsa ya ƙara buɗewa, abinda ba zan iya tabbatarwa ba ko wannan lokacin zai banbanta. Ya gaya wa na kusa da shi zai fitar da kuɗi lokacin da ya dace."
Mataimakin shugaban matasan PDP, Timothy Osadolor, yace gwamnan Edo Godwin Obaseki, na kokari iyakar iyawarsa yana samar da kuɗaɗe ga kwamitin kamfe na jiharsa.
"Ba zan ari bakin wasu gwamnoni na ci musu albasa ba amma gwamna Obaseki yana kokari, mai yuwuwa akwai wasu takwarorinsa da ban sani ba, duk wasu harkokin kamfe jihar ke samar da su."
Menene gaskiyar shugabna kwamitin Kamfe na shirin murabus kan rashin kudi?
A ranar Talata, jam'iyyar PDP ta musanta rahoton dake cewa shugaban kwamitin kamfen shugaban ƙasa, Gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom na barazanar yin murabus sakamkon rashin isassun kuɗi.
Da yake zantawa da Punch ta bayan fage kan rahoton, kakakin PDP na ƙasa, Debo Ologunagba, yace:
"Rahoton ƙarya ne, bai yi kama da gaskiya ba kuma wasu mutane ne kawai suka ƙirƙira, shi kansa gwamna Emmanuel ya musanta labarin."
Haka zalika a wata hira ta daban, kakakin kwamitin yaƙin Atiku/Okowa kuma kwamishinan yaɗa labarai na jihar Delta, Charles Aniagwu, yace rahoton babu isassun kuɗi ba gaskiya bane.
Ibrahim Tsauri, mamba a kwamitin zartaswa na PDP ta ƙasa (NEC) yace idan har gwamna Emmanuel ya yi korafin karancin kudi, "Tabbas akwai matsala."
Yace, "Idan har dagaske shugaban tawagar kamfe ya koka kan rashin kuɗi, to fa akwai matsala. Kamfe yana bukatar kuɗi ba kaɗan ba domin waɗanda zasu riƙa zagaye kasar nan ba a mota zasu je ba, jirgi zasu nema."
"Mai yuwuwa Udom ya koka ne kan kuɗin da aka ware sun yi kaɗan kuma da gaskiyarsa ya kamata a duba."
A wani labarin kuma Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammed, ya nuna damuwarsa kan yadda tawagar kamfen PDP ya ware shi
Wata Sabuwa a APC, Wani Babban Jigo da Wasu Shugabanni Sun Ayyana Goyom Baya Ga Ɗan Takarar PDP a 2023
A wata wasika mai ɗauke da sa hannunsa da sauran masu faɗa aji na PDP a Bauchi, Muhammed ya koka kan yadda ake tafiyar da harkoki ba tare da nemansa ba.
Yace Atiku Abubakar ya ɗauki wasu tsirarun mutane yana goya musu baya, su kuma suna abinda suka ga dama.
Asali: Legit.ng