Zaben 2023: Zan Fatattaki Bala Mohammed Daga Kujerar Mulki, Dan Takarar Gwamna Na NNPP

Zaben 2023: Zan Fatattaki Bala Mohammed Daga Kujerar Mulki, Dan Takarar Gwamna Na NNPP

  • Sanata Halliru Jika, dan takarar gwamna na jam'iyyar NNPP a jihar Bauchi a zaben 2023 ya ce zai kayar da gwamna Bala Mohammed
  • Jika ya yi watsi da rahotannin da ke yawo a soshiyal midiya na cewa yana yi wa dan takarar gwamna na APC a jihar aiki
  • Sanata Jika ya ce tsoron karbuwa da ya samu a wurin mutanen Bauchi ne yasa wasu ke masa makirci da bita da kulli

Bauchi - Dan takarar gwamna na jam'iyyar New Nigeria's Peoples Party, NNPP, a jihar Bauch, Sanata Halliru Jika, ya sha alwashin kayar da gwamnan jihar mai ci, Bala Mohammed, a zaben da ke tafe.

Ya bayyana rahotannin da ke cewa shi dan bata kuri'a ne a matsayin makirci, Daily Trust ta rahoto.

Bauchi Map
2023: Zan Fatattaki Bala Mohammed Daga Kujerar Mulki, Dan Takarar Gwamna Na NNPP. Hoto: @daily_trust.
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Dan Takarar Gwamnan PDP a Zamfara Ya Fusata, Ya Yi Kakkausan Martani Kan Hukuncin Kotu

Jika, wanda a yanzu ya ke wakiltar Bauchi Central a Majalisar Dattawa, ya ce ya yanke shawarar yin takarar gwamna ne a 2023 don sauya tsarin siyasar jihar da kawo romon demokradiyya ga mutanen jihar.

Sanatan, wanda ya bayyana hakan wurin taron da aka yi a filin kwallo na Railway a Bauchi inda ya tarbi wadanda suka shigo jam'iyyar ta NNPP, ya ce PDP da APC duk hantsarsu na kadawa saboda takararsa, rahoton HeadTopics Nigeria.

Karya ne, bana yi wa dan takarar APC aiki, In ji Sanata Jika

Jika ya ce:

"Bari in gyara wani mugunyar bayani da ke yawo a soshiyal midiya cewa ina yi wa wani aiki ne. Sun san ni sosai da tarihin siyasa ta a cikin Bauchi da wajenta.
"Ni ba rago bane a siyasar Bauchi kuma ni dan asalin jihar ne wanda ya bada gudunmawa don cigabar jihar. Saboda kishin karbuwa ta, sun koma yi min bita da kulli da cewa dan takarar APC na ke yi wa aiki.

Kara karanta wannan

Atiku Yana Da Tambayoyi Da Zai Amsa Kan Alakarsa Da Yan Ta'adda, In Ji Fani-Kayode

"Ina son in fayyace cewa ina takara ne don kayar da gwamna Bala Mohammed da biya wa mutanen Bauchi musamman matasa da mata bukatunsu saboda goyon baya da suka bamu tunda muka fara wannan tafiyar."

Daga karshe ya ce a hadu a wurin zabe a dena rudar mutane da maganganu marasa tushe domin abin da ke gabansa shine kawo canji a Bauchi don mutanen Bauchi sun yanke shawarar zaben cancanta a maimakon makaryata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel