Atiku, Kwankwaso Ko Obi? APC Ta Fadi Dan Takara 1 Da Zai Fafata da Tinubu, Tace Sauran Cikon Benci Ne
- Hannatu Musawa, mataimakiyar kakakin APC, ta ce da Atiku Abubakar na PDP kadai jam’iyyar ke takarar shugabancin kasa a 2023
- Musawa ta bugi kirji cewa dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, zai lallasa Atiku da tazara mai yawa a zaben 2023
- Jigon ta APC ta jadadda cewa NNPP da Labour Party duk yan cikon benci ne domin basu da tsari ko karfi a siyasance
Abuja – Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta ce zaben shugaban kasa na 2023 zai kasance tsere ne tsakanin mutane biyu wato dan takararta na shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da takwaransa na Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar.
Da take magana kan zaben, mataimakiyar kakakin kungiyar yakin neman zaben shugabancin Tinubu/Shettima, Hannatu Musawa, ta ce kamar yadda yake a kundin tsari, jam’iyyar Labour Party ba za ta iya lashe zaben shugaban kasa na 2023 ba saboda yaduwarta, Leadership ta rahoto.
2023: Tinubu Ya Fi Duk Sauran Yan Takarar Shugaban Kasa Cikakken Lafiya – Kungiyar Yakin Neman Zaben APC
Jigon APC ta yi watsi da Peter Obi a zaben na 2023
Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, ya shahara sosai a tsakanin matasa musamman ma a shafukan soshiyal midiya, kuma ana ta hasashen zai iya lashe zaben.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai Musawa ta ce Tinubu zai lashe zaben yayin da Aiku zai zo na biyu da tazara mai yawa. Ta kara da cewar jam’iyyun Labour Party, New Nigeria Peoples na Rabiu Kwankwaso da sauransu duk yan cikon benci ne da za su amfani tsarin.
Hannatu ta bayyana cewa zaben shugaban kasa na 2023 don Tinubu ya lallasa Atiku na PDP ne da tazara mai yawa.
Atiku Abubakar na PDP, Asiwaju Bola Tinubu na APC, Peter Obi na Labour Party da Rabiu Kwankwaso na NNPP
Ta bayyana hakan ne a Abuja a ranar Talata, 8 ga watan Nuwamba, yayin da take jadadda matsayinta kan yaduwa APC da kuma tanadin da jam’iyyar ta yiwa yan Najeriya wanda Tinubu ya gabatar da wata takarda.
Wani bangare na jawabinta na cewa:
“Don haka, ina iya cewa PDP ce babbar abokiyar adawa. Ga Labour Party, ba za ta taba iya cin zabe ba a kundin tsarin mulki.”
Asali: Legit.ng