Atiku Yana Da Tambayoyi Da Zai Amsa Kan Alakarsa Da Yan Ta'adda, In Ji Fani-Kayode

Atiku Yana Da Tambayoyi Da Zai Amsa Kan Alakarsa Da Yan Ta'adda, In Ji Fani-Kayode

  • Bisa ga dukkan alamu Femi Fani-Kayode baya kakkautawa a hare-haren da ya ke yi wa dan takarar shugaban kasa na PDP
  • Kwana guda bayan cewa tsohon mataimakin shugaban kasar bai samu goyon bayan gwamnonin PDP ba, Fani-Kayode ya alkanta Atiku da yan ta'adda
  • A yayin da ya ke maimaita kalaman Ortom a kan Atiku, Fan-Kayode ya bayyana cewa ya kamata a binciki dan takarar shugaban kasar

Twitter - Femi Fani-Kayode, mamba na kwamitin yakin neman zabe na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ya yi ikirarin cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, na da alaka da yan ta'adda.

Dan siyasan haifafan jihar Osun ya yi wannan zargin ne a rubutun da ya yi a Tuwita a ranar Talata, 8 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Shugaban Yakin Neman Zaben Atiku Zai 'Ajiye' Aiki Saboda Karancin Kudin Kamfe

Fani Kayode
Atiku Yana Da Tambayoyi Da Zai Amsa Kan Alakarsa Da Yan Ta'adda, In Ji Fani-Kayode. Hoto: Femi Fani-Kayode.
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya rubuta:

"Gwamna Ortom ya yi magana mai daci game da Atiku. Akwai tambayoyin da Waziri zai amsa game da alakarsa da yan ta'adda da suka kashe mutane da dama wadanda ba su ji ba ba su gani ba a arewa.
"Kowanne dan ta'adda yana da mai daukan nauyinsa. Akwai bukatar a bincika alakar Waziri da 'dillalan mutuwa'."

Idan za a iya tunawa, a ranar Litinin 7 ga watan Nuwamba, Fani-Kayode ya kuma wallafa sako na tsokanar Atiku, yana mai ikirarin cewa dan takarar shugaban kasar na PDP ya gaza iya tafiyar da jam'iyyar.

Ya rubuta:

"Ka rasa Wike, Makinde, Ortom, Ikpeazu, Ugwuanyi kuma yanzu Bala Mohammed. A maimakon ta tuntube su ka aika saurayin 'mai bilicin kuma dan daba' zuwa taron jin ra'ayin mutane ya ci razana tare da cin mutuncin Peter Obi.

Kara karanta wannan

Za mu zama marasa amfani idan muka bari Tinubu yaci zabe, Kiristocin Arewa

"Waziri, rayuwarka na tabarbarewa!".

Abin Da Wike Ya Fada Wa Atiku A Sabuwar Ganawar Da Suka Yi Kan Rikicin PDP

A kokarin warware rikicin jam'iyyar PDP, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya sake ganawa da Gwamna Mr Nyesom Wike na Jihar Rivers.

Wata majiya da ta halarci taron ta fada wa Daily Trust cewa wasu hadiminan bangarorin biyu sun halarci taron.

An yi ganawar ne a gidan gwamnatin Rivers da ke Asokoro a birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164