PDP Tayi Karar ‘Dan Takaran APC a Kotu, Ta Kawo Hujjar da Za ta Iya Hana Shi Mulki
- Takarar Gwamnan jihar Ribas da jam’iyyar APC take shirin yi a zabe mai zuwa ta gamu da cikas
- Jam’iyyar PDP mai rike da Ribas tace akwai matsala tattare da takarar Tonye Cole a zaben 2023
- Lauyoyin PDP sun ce Cole yana da takardar zama mutumin Ingila, wanda ya ci karo da doka
Rivers - A ranar 24 ga watan Nuwamban 2022, Tonye Cole zai san matsayarsa game da takarar gwamna da yake neman yi a jihar Ribas a zabe mai zuwa.
PM News ta fitar da rahoto a ranar Litinin cewa an shigar da Tonye Cole da nufin a hana shi neman zama Gwamnan jihar Ribas a karkashin jam’iyyar APC.
Jam’iyyar PDP mai mulkin Ribas da ta shigar da karar, tana ikirarin cewa ‘dan takaran yana da katin shaidar zama ‘dan wata kasa dabam da Najeriya.
Wata Sabuwa a APC, Wani Babban Jigo da Wasu Shugabanni Sun Ayyana Goyom Baya Ga Ɗan Takarar PDP a 2023
Rahoton yace PDP ta na so a rusa takarar Cole saboda yana da takardar zama mutumin Birtaniya. Sai a karshen watan nan ne za a saurari shari'ar.
Za a sake shari'a da Obile
Sauran wadanda jam’iyyar ta hada a kotu a wannan shari’a sun hada da jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya da kuma hukumar zabe na kasa watau INEC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Karar da aka kai Arch. Tonye Cole ta na gaban Mai shari’a Emmanuel Obile na babban kotun tarayya II mai zama a garin Fatakwal da ke jihar Ribas.
Kakakin kwamitin yakin neman zaben Tonye Cole/Innocent Barikor 2023, ya tabbatar da cewa jam’iyyar PDP za tayi shari’a da ‘dan takaransu a kotu.
An kai mu kotu - Kwamitin kamfe
Rahoton Daily Post yace Mr. Sogbeye C. Eli ya shaidawa manema labarai cewa PDP tana so a hana Cole yin takara domin ba Najeriya ce kadai kasar shi ba.
A madadin kwamitin Tonye Cole/Innocent Barikor a zaben 2023, C. Eli ya tabbatarwa manema labarai masu karar su na ikirarin Cole ba zai iya shiga zabe ba.
Alkali Obile shi ne wanda ya ruguza takarar duk wani ‘dan APC da ya samu tuta a jihar Ribas.
Minista v 'Yan Majalisa
An samu rahoto ‘Yan Majalisar Wakilai daga jihohin Bayelsa, Ribas, Delta, Kuros Ribas, Edo da Akwa Ibom ba su ji dadin maganar Sadiyar Farouk ba.
Hon. Sadiya Farouq tace a duk inda aka yi ambaliyar ruwa a shekarar nan, babu inda abin ya yi kamari irin jihar Jigawa, wannan ya fusata ‘yan majalisar.
Asali: Legit.ng