A Kotu Zan Tabbatar da Ni Na Yi Nasara a Zaben da Aka Gudanar, in Ji Gwamnan Osun Oyetola
- Gwamnan jihar Osun ya bayyana tafiya kotu don tabbatar da shi ya yi nasara a zaben da aka gudanar a jihar
- An yi zabe a watan Yuli a Osun, an ayyana dan takarar jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben
- Oyetola ya yi alkawarin kawo kuri'u ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu
FCT, Abuja - Gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola ya bayyana kwarin gwiwarsa game da samun nasara a kotu mai zama kan zaben gwamnan da aka gudanar.
Jam'iyyar APC a watan Agustan bana ta bayyana cewa, za ta kalubalanci zaben da aka gudanar a jihar Osun a watannin baya, TheCable ta ruwaito.
Ademola Adeleke, dan takarar gwamnan jam'iyyar PDP ne ya lashe zaben da aka gudanar a jihar a ranar 16 ga watan Yuli.
Adeleke ya samu kuri'u 403,371, inda ya kada abokin hamayyarsa Gboyega Oyetola na APC mai kuri'u 375,027 a zaben.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gboyega Famodun, shugaban APC na Osun ya bayyana cewa, duba da shawarin da lauyoyin APC suka bayar, suna da kwarin gwiwar samun nasara a kotu a kalubalantar sakamakon zaben.
Da yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin a Abuja yayin wata ziyara da ya kai, gwamnan na Osun ya ce bai da matsala kan shiga kotu don tabbatar da burinsa.
Za mu ba Tinubu kuri'i miliyan 1 a 2023, inji Oyetola
Ya kuma bayyana cewa, yana da kwarin gwiwar Tinubu zai samu kuri'u miliyan daya a jiharsa ta Osun, rahoton Vanguard.
Ya ce:
"Bani da wata fargaba. Na yi imani da Allah. Zan dawo da hakkina.
"Mun fara gangamin kamfen. Makon da ya gabata, mun yi gangamin nuna goyon baya a zagayen jihar. Mun yi tattakin kilomita 11.
2023: Wike Da Wasu Gwamnoni 4 Da Suke Fushi Da PDP Sun Hada Kai Da Tinubu, Ortom Ya Rungumi Peter Obi
"Sakamakon ya haifar da da mai ido. Osun dai a kullum jiha ce ta APC. Don haka, babu wani abin damuwa a kai. Zan iya tabbatar muku, za mu kawo kuri'u ban da kasa da miliyan daya ga Asiwaju."
Kotun Jos Ta Yanke Wa Mai Gadi Hukuncin Daurin Watanni Shida Bisa Laifin Barci a Bakin Aiki
A wani labarin, wata kotun yanki a birnin Jos ta jihar Filato ta daure wani mai gadi, Abubakar Haruna a magarkama na tsawon watanni shida a ranar Litinin bisa kama shi da laifin sharbar barci a bakin aiki.
Rahoton da muka samo daga jaridar Vanguard ya ce, barcin da Abubakar ya yi ya kai ga shigowar barayi har suka saci karafan rodi da kwanon rufin gida.
Alkalan da suka yanke hukuncin, Malam Sadiq Adam da Mr Hyacenth Dolnanan sun yi hakan ne bayan da ya amsa laifinsa na yin sakaci da aikin da aka ba shi.
Asali: Legit.ng