2023: Ambaliyar Wutar Rikici Ma Jiran PDP Nan Gaba, Fayose
- Tsohon gwamnan jihar Ekiti dake goyon bayan tsagin Wike ya yi hasashen cewa akwai babban rikici mai muni dake tunkaro PDP
- Ayodele Fayose, yace yana ba masu ruwa da tsaki shawarin su ɗauki matakai tun gabanin abun ya ci karfinsu
- Gwamnan jihar Ribas da wasu gwamnoni huɗu sun matsa tilas shugaban PDP na ƙasa ya yi murabus
Ekiti - Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, yace wannan rikicin da jam'iyyar PDP ke fama da shi somin taɓi ne, nan gaba zata shaida tulin matsala.
Mista Fayose ya yi wannan hasahen ne a wani rubutu da ya saki a shafinsa na ɗandalin sada zumunta watau Tuwita.
A cewar Fayose, dambarwar da ta hana jam'iyyar PDP zaman lafiya ka iya ƙara tsananta matuƙar ba'a gaggauta shawo kan saɓanin dake akwai ba yanzu haka.
Wata Sabuwa a APC, Wani Babban Jigo da Wasu Shugabanni Sun Ayyana Goyom Baya Ga Ɗan Takarar PDP a 2023
A rubutun da ya saki a Tuwita, Fayose yace:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"ina hango babbar ambaliyar rikici nan gaba a jam'iyyar PDP wanda ba'a taɓa ganin irinsa ba. Na yi shiru da baki na tsawon lokacin la'alla ko abubuwa zasu gyaru."
"Ina mai ba kanmu shawara mu ƙara zage dantse wurin warware wannan rikicin domin a kullum kwana batun ƙara tsananta yake. Ina fatan ba za'a yi fatali da wannan shawarin ba."
Idan baku manta ba, Fayose ya nemi tikitin takara a zaɓen fidda gwanin jam'iyyar PDP da ya gudana a watan Mayu amma ya sha kaye a hannun Atiku Abubakar.
A watan Satumba, Tsohon gwamnan yace duk da yana tare da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, zai yi wa ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku aiki a zaɓe mai zuwa.
Wike ya jima yana takun saƙa da Atiku Abubakar, da kuma shugaban PDP na ƙasa Iyorchia Ayu tsawon watanni, ya tsaya tsayin daka cewa ba ta yadda yan arewa zasu lamushe manyan mukaman biyu.
A wani labarin kuma Bidiyon Yadda Peter Obi Ya Fusata, Ya Takali Kakakin Atiku a Wurin Mahawarar Yan Takara
Wani abu tamkar wasan kwaikwayo ya faru a wurin taron da aka shiryawa yan takarar shugaban kasa tsakanin Obi da Melaye.
Lamarin dai wanda ya fara daga surutun da aka jiyo wani na yi, Peter Obi, ya nuna fushinsa kan dora laifin kan mutanensa.
Asali: Legit.ng