Yaron Gwamnan APC Ya Yarda Kwankwaso Barazana ne a Takarar Shugaban Kasa

Yaron Gwamnan APC Ya Yarda Kwankwaso Barazana ne a Takarar Shugaban Kasa

A ra’ayin Bashir El-Rufai, Rabiu Musa Kwankwaso zai iya kawowa jam’iyyu cikas a zabe mai zuwa

Yaron Gwamnan na Kaduna ya yi magana a dandalin Twitter, yace ‘Dan takaran zai iya bata lissafi

Masu tofa albarkacin bakinsu su na tayi tun da ‘Dan takaran ya je muhawarar da aka shirya a jiya

Kaduna - Bashir El-Rufai wanda mahaifinsa shi ne gwamnan jihar Kaduna, ya tofa albarkacin bakinsa a game da siyasar Najeriya.

Malam Bashir El-Rufai ya yi magana a kan Rabiu Musa Kwankwaso shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 6 ga watan Oktoba 2022.

Hadimin ‘dan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazabar Kaduna ta Kudu ya jawo muhawara a shafin sada zumuntan zamanin.

“Na maimaita, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso barazana ne.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: Jigo Ya Gargadi Jam’iyya, Yace ‘Dan Takaran Kano Yana Tare da Atiku

- Bashir El-Rufai

Ina ma dai a ce...

Nan-take wani masani, A.I. Adamu, PhD ya bada amsa da cewa ina ma a ce Kwankwaso yana takara ne a wata babbar jam’iyya.

Shi ma Bashir El-Rufai ya yarda da wannan ra’ayi, yace ‘dan siyasar zai iya zama magajin Muhammadu Buhari a jam’iyya mai suna.

Rabiu Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso da Peter Obi Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter
“Na yarda kwarai Dr. Tana iya yiwuwa ya zama kamar wani Buhari, mai dinbin magoya baya a tafiyar siyasa.”

- Bashir El-Rufai

Amma wasu sun maida martani su na cewa tasirin tsohon gwamnan na jihar Kano a zaben shugaban kasa ba zai wuce jihar Kano ba.

Shi kuwa matashin yace Kwankwaso zai iya kawowa duk wata jam’iyya cikas a Kano, kuma tasirinsa ba zai wuce yankin na sa ba.

Amma duk da haka, Bashir El-Rufai yace ko da a haka aka tsaya, za a ga canji a 2023.

Inda NNPP za tayi barna

Wani Abubakar Sadiq yace ko da Rabiu Kwankwaso ba zai kai labari ba, yana ganin zai yi nasara a jihohin Kano, Katsina, da Jigawa.

Kara karanta wannan

Rabiu Kwankwaso Ya Zauna da Jakadun Kasashe 25, Ya Bayyana Dalilin Haduwarsu

Dr. Abdul Muiz yana ganin ana zuzuta ‘dan takaran, yace a zaben 2019 shi da PDP ba su iya tsira da kujerar Sanata ko daya a Kano ba.

Muhawarar 'yan takara

An ji labari cewa Arise TV da Cibiyar CDD sun shirya wata tattaunawar muhawara da masu neman mulkin Najeriya a zaben mai zuwa.

Ifeanyi Okowa ne ya wakilci Atiku Abubakar yayin da Bola Tinubu bai iya zuwa ba, amma kwamitin kamfensa ya jero uzurorinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel