2023: APC ta Tarbi Fiye Da Mutum 1000 Da Suka Sauya Sheka Daga PDP A Zamfara

2023: APC ta Tarbi Fiye Da Mutum 1000 Da Suka Sauya Sheka Daga PDP A Zamfara

  • Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta yi sabbin mambobi fiye da 1,000 gabannin babban zaben 2023
  • Tsohuwar shugabar matan PDP a jihar Zamfara, Hajiya Madina Shehu ce ta jagoranci tawagar masu sauya shekar
  • Gwamna Bello Matawalle ya bayyana wannan ci gaban a matsayin babban kamu ga jam'iyyar mai mulki

Zamfara - Shugabar matar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Zamfara, Hajiya Madina Shehu, ta sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

PM News ta rahoto cewa Madina Shehu ta sanar da sauya shekar tata ne a ranar Alhamis bayan wata ganawa da tayi da Gwamna Bello Matawalle a Gusau, babban birnin jihar ta Zamfara.

PDP da APC
2023: APC ta Tarbi Fiye Da Mutum 1000 Da Suka Sauya Sheka Daga PDP A Zamfara Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Ta bayyana cewa bar PDP ne saboda rashin tsari na shugabanci a cikin jam’iyyar.

“Ina sanar da sauya shekata zuwa APC tare da shugabannin mata na PDP a kananan hukumomi 14 na jihar.”

Kara karanta wannan

PDP ta rasa kuri'un matan Zamfara, shugabar mata ta sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake martani, Matawalle ya bayyana sauya shekar Shehu a matsayin ci gaba mai kyau ga jam’iyyar APC a jihar.

“Akwai Karin masu sauya sheka da ke zuwa APC daga PDP, kwanan nan zamu samu karin mambobin PDP da dama ciki harda shugabanninsu.”

Matawalle ya kuma ce babban abokin adawarsa, Dr Dauda Lawal Dare, sabon shiga ne a siyasa wanda bayan zaben 2023 zai tsorata sannan ya nemi mabuya da zaran ya ji batun takarar siyasa saboda sais ha gagarumin kaye a zaben, rahoton Punch.

Babu Shugaban Kasa Irin Buhari A Tarihin Najeriya – Kakakin APC

A wani labarin, mun ji cewa sakataren labarai na jam'iyyar APC a jihar Zamfara, Alhaji Yusuf Idris, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi abubuwan da ya cancanci a yaba masa a kasar nan.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Daukarwa Al’ummar Kogi Gagarumin Alkawari Gabannin Zaben 2023

A cewar kakakin na APC, ba a taba shugaban kasa irin Muhammadu Buhari a tarihin Najeriya, Jaridar Vanguard ta rahoto.

Idris ya fada ma kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Abuja cewa shugaban kasar yayi namijin kokari a shekaru bakwai da suka gabata.

"Sai dai, ya zama dole a kara wayarwa jama'a da kai kan tsare-tsare da manufofI da kuma nasarorin gwamnatin Buhari."

Idris ya bayyana cewa a tarihin shugabancin Najeriya, Buhari ne kadai ya kaddamar da shirin zuba jari da ke da manufofi iri-iri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng