Tsohuwar Kwamishina a Jihar Ribas Ta Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP

Tsohuwar Kwamishina a Jihar Ribas Ta Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP

  • Tsohuwar shugabar hukumar NDDC data fice APC tun watan Yuli, Ibim Semenitari, ta shiga jam'iyyar PDP a jihar Ribas
  • Semenitari, tsohuwar kwamishina a mulkin Amaechi, tace dama PDP ce gidanta na farko a siyasa
  • Rikicin cikin gida ya dabaibaye jam'iyyar APC a jihar Ribas karkashin jagorancin tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi

Rivers - Tsohuwar kwamishinar yaɗa labarai da sadarwa a jihar Ribas kuma tsohuwar shugabar hukumar raya Neja Delta ta riko, Ibim Semenitari, ta rungumi jam'iyyar PDP.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Semenitari, wanda ta kasance yar amutun tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ta fice daga jam'iyyar APC ne tun a watan Yuli 2022.

APC a jihar Ribas.
Tsohuwar Kwamishina a Jihar Ribas Ta Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP Hoto: punchng
Asali: UGC

Amma tun wancen lokaci, Semenitari, ta ɓoye inda ta nufa a siyasance kafin yanzu da ta tabbatar da shiga jam'iyyar PDP mai mulkin jihar Ribas.

Kara karanta wannan

2023: Jerin Makusantan Amaechi Da Suka Fice Daga APC Suka Koma Wurin Wike A PDP Ta Jihar Ribas

A ranar Asabar, Semenitari ta samu kyakkyawar maraba daga shugaban ƙaramar hukumar Okrika, Akuro Tobin, tsohon kwamishinan lafiya, Dr. Sampson Parker, da wasu jiga-jigan PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar 10 ga watan Yuli, 2022, tsohuwar shugabar NDDC ta fice daga APC bayan miƙa wasika ga shugaban APC na gunduma ta 5, ƙaramar hukumar Okrika, jihar Ribas.

Duk da dai bata bayyana abinda ya rinjayeta harta dauki wannan matakin ba amma ana ganin ba zai rasa alaƙa da rikicin cikin gida da ya haddasa murabus da sauya shekar 'ya'yan APC reshen jihar karkashin Amaechi ba.

Meyasa ta zaɓi komawa PDP?

Game da batun shiga jam'iyyar PDP, Semenitari, ta shaida wa manema labarai cewa dama can jam'iyya mai mulkin Ribas ce asalin gidanta na fari, kamar yadda the nation ta ruwaito.

A kalamanta tace:

"Gidana na farko a siyasa ita ce PDP, na barta ne tare da tsohon shugaba na (Rotimi Amaechi) wanda shi ne jagora a wancan lokacin a Ribas kafin daga bisani ta subuce daga hannunsa."

Kara karanta wannan

Rikici Na Kara Tarwatsa PDP, Atiku Ya Yi Rashin Babbar Jigo a Jihar Gombe

"Wajibi kowace siyasa ta amfanar da mutane, na fita daga APC ne a karan kaina, na gaza gamsar da masoyana da kuma waɗanda ke ganin dole su zauna a inuwar APC saboda ni."

A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP Ta Dare Gida Biyu a Jihar Arewa, Ta Dakatar da Ɗan Takarar Gwamna a 2023

Jam'iyyar PDP ta sake shiga sabon rikici a jihar Katsina, mutum biyu na ikirarin shugabancin jam'iyyar.

Tsagin Alhaji Majigiri dake samun goyon baya daga Ibrahim Shema, sun sanar da dakatar da ɗan takarar gwamna Yakubu Lado.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262