Bayan Shekara 7 Yana Kan Kujera, Da Bakinsa, Minista Yace Bai Tabuka Komai Ba
- Ministan ilmi na Najeriya, ya gamsu bai tabuka abin kirki duk da tsawon damar da ya samu ba
- Mallam Adamu Adamu shi ne wanda ya fi kowa dadewa a tarihi yana rike da ma’aikatar ilmi
- Da aka je taron NCE a Abuja, Adamu ya gabatar da jawabi, yana mai cewa ya gaza a matsayin Minista
Abuja - Ministan ilmi na kasa, Mallam Adamu Adamu, ya fito yana cewa ya gaza a matsayinsa na wanda ma’aikatar tarayya take hannunsa.
Mai girma Ministan ya bayyana cewa ya gagara shawo kan tulin matsalolin da ake fama da su a bangaren ilmi, Sun ta kawo wannan rahoto.
A tarihin Najeriya, babu wanda ya dade a kan kujerar Ministan ilmi irin Adamu Adamu, tun a watan Nuwamban 2015 aka rantsar da shi.
Dadewar da Ministan ya yi yana jagorantar bangaren ilmi, bai kawo cigaban da aka yi tunani ba.
Matsaloli sun karu a Najeriya
Mallam Adamu Adamu yace a lokacinsa ne adadin yaran da ba su zuwa makaranta a Najeriya suka kara yawa, a maimakona adadin ya ragu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Bugu da kari, Ministan yace bai iya kawo mafita a kan yadda za a shawo karshen yajin-aikin da malamin jami’a ke yawan yi a Najeriya ba.
Karatun gaba da sakandare yana fama da kalubale iri-iri a kasar nan, Ministan ilmin ya yarda cewa bai yi nasarar magance wadannan matsaloli ba.
Jaridar tace babban Ministan ya yi wannan jawabi ne a wajen taron majalisar ilmi ta kasa watau NCE wanda aka gudanar a birnin tarayya Abuja.
Da laifin Jihohi - Adamu
Da yake bayani a ranar Alhamis, 3 ga watan Nuwamba 2022, Adamu Adamu ya nuna jihohi sun taimaka masa wajen rashin nasarar da ya samu.
Nauyin karatun matakin firamare ya rataya ne a kan wuyan gwamnoni, yayin da gwamnatin tarayya ke daukar nauyin tun daga sakandare.
Kafin zamansa Minista a 2015, ‘dan jaridar ya yi ta rubutu da sharhi, yana kawo mafitar yadda malaman jami’a za su daina zuwa yajin-aiki.
Yajin aikin ASUU
An yi ta fama da yajin-aiki iri-iri daga kungiyar ASUU a gwamnatin nan. Sai kwanan nan aka ji babban kotun daukaka kara ta umarci a koma aiki.
Kafin nan an shafe watanni kusan takwas a gida ba tare da an iya ci ma matsaya tsakanin gwamnatin Muhammadu Buhari da 'yan ASUU ba.
Asali: Legit.ng