Yanzu-Yanzu: Gwamnonin APC 5 Na Tattaunawa da Atiku Abubakar

Yanzu-Yanzu: Gwamnonin APC 5 Na Tattaunawa da Atiku Abubakar

  • Babbar jam'iyyar PDP mai adawa a kasar ta ce gwamnonin APC biyar na kan tattaunawa da dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar
  • Kakakin kungiyar yakin neman zaben Atiku, Kola Ologbondiyan, ya ce burin APC da Bola Tinubu na cin gajiyar rikicin PDP ba zai yi tasiri ba
  • Ologbondiyan ya ce jam'iyya mai mulki a kasar za ta sha mamaki da ganin yadda abubuwa za su juya gabannin zaben 2023

Jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) ta ce gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) 5 na cikin tattaunawa da dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar, Kola Ologbondiyan ne ya bayyana hakan a wata hira da jaridar Daily Independent, a ranar Alhamis, 3 ga watan Nuwamba.

Atiku Abubakar
Yanzu-Yanzu: Gwamnonin APC 5 Na Tattaunawa da Atiku Abubakar Hoto: Independent
Asali: Facebook

Ya kuma bayyana cewa kudirin APC da dan takararta na shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu na ci daga rikicin da ke tsakanin Atiku da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ba zai cimma nasara ba.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jam'iyyar APC Ta Saki Jadawalin Yakin Neman Zabenta Na Shugaban Kasa

Karamin ministan kwadago kuma kakakin kungiyar yakin neman zaben Tinubu da Shettima ya bayyana a baya cewa fusatattun jiga-jigan PDP za su marawa takarar shugabancin Tinubu baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma ce baya ga Wike da hadimansa, sauran gwamnonin PDP basa bayan Atiku.

Yayin da yake martani ga ikirarin Keyamo, Ologbondiyan, tsohon sakataren labaran PDP na kasa ya ce jawabin ba gaskiya bane.

“Ba wai bamu da masaniya kan fata da rawar ganin da APC da dan takararta na shugaban kasa ke takawa ba a kokarinsu na ci daga sabanin da ke jam’iyyarmu.
“Amma kada su damu saboda akallka gwamnoni biyar da aka zaba karkashin inuwar APC ne ke tattaunawa da PDP da dan takararta na shugaban kasa.
“Shakka babu so suke su amfana daga lamarin amma za su hadu da tangarda.”

Kara karanta wannan

PDP ga Shettima: Cutar Mantau Ke Damunka, Gidanku Yana Ci da Wuta, Ku Fara Magance shi

Gwamna Ganduje Ya Roki Al'ummar Hausawa Su Taimaka Su Zabi Tinubu/Shettima a 2023

A wani labarin, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci al’ummar Hausa-Fulani mazauna jihar Kano da su marawa dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu da mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima baya a zaben 2023.

Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin wata ziyara da ya kaiwa al’ummar arewa a Alaba Rago da ke yankin Ojo na jihar, jaridar Punch ta rahoto. Ya kuma samu rakiyar Shettima da gwamnan jihar Lagas, Babajide Sanwo-Olu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng