Yanzu-Yanzu: Wani Ministan Buhari Ya Amince da Cewa Ya Gaza a Matsayin Minista

Yanzu-Yanzu: Wani Ministan Buhari Ya Amince da Cewa Ya Gaza a Matsayin Minista

  • A ranar Alhamis, 3 ga watan Nuwamba, ministan ilimi, Mallam Adamu Adamu, ya yarda cewa ya gaza a ma’aikatarsa
  • Adamu, ya bayyana a taron NCE karo na 66 cewa bai yi nasarar magance matsalolin da ma’aikatar ke fuskanta ba
  • Ministan ya bayyana cewa karuwar yawan yaran da basa zuwa makaranta da yajin aikin ASUU na cikin gazawarsa

Abuja - Ministan ilimi, Mallam Adamu Adamu, ya yarda cewa ya gaza a matsayinsa na minista domin ya kasa magance matsaloli da dama da yakamata ace ya magance.

Adamu wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 3 ga watan Nuwamba ya ce ya gaza warware tarin matsaloli duk da kasancewarsa ministan ilimi mafi dadewa, jaridar The Sun ta rahoto.

Adamu Adamu
Yanzu-Yanzu: Wani Ministan Buhari Ya Amince da Cewa Ya Gaza a Matsayin Minista
Asali: UGC

Ministan ya jero cewa ya gaza samar da mafitar da ake bukata kama daga kan yawan yaran da basa zuwa makaranta wanda adadinsu ya karu a karkashinsa zuwa ga matsalar ASUU da sauran matsaloli da ke addabar tsarin ilimin jami'a.

Kara karanta wannan

Mummunar Ambaliya Ta Kori Sarki, Mai martaba Ya Koma Kwana Cikin Mota

Ministan wanda yayi jawabi a taron kwamitin ilimi na kasa (NCE) a Abuja, ya kuma zargi ma'aikatun ilimi na jiha da kara ta'azzara abubuwan da suka taimaka wajen gazawarsa a matsayin minista.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mun Yi Duk Mai Yiwuwa Don Ganin Mun Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU, Gwamnatin Buhari

A wani labarin, mun ji cewa bayan da aka shafe watanni ana kai ruwa rana a batun yajin aikin ASUU, gwamnatin Buhari a ranar Talata ta ce ta yi iyakar kokarinta don ganin ta kawo karshen rikicin gwamnati da kungiyar malaman jami'o'i.

Wannan na fitowa ne daga bakin ministan ilimi, Adamu Adamu a wata ganawa da ake yi da shugabannin jami’o’in tarayya da hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) a Abuja.

Ya zuwa yanzu dai da rahoton nan ke shigowa mana daga jaridar The Nation, an ce manyan jami'an na gwamnati suna cikin ganawar sirri.

Kara karanta wannan

Soyayya Ta Gaskiya: Bidiyon Yadda Ango Ya Goyo Amaryarsa A Babur Zuwa Wajen Daurin Aurensu Ya Ja Hankali

Ana sa ran minista Adamu zai yi wa manema labarai bayani da zarar an kammala ganawar.

Minista Adamu ya batu daga shugaba Buhari na kan matsayar cewa, duk da ana kokarin malamai su koma bakin aiki, amma ba za a maimaita kuskuren rubuta wata yarjejeniya da ba za ta haifar da da mai ido ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel