Fusatattun Yan Takarar da Suka Sha Kaye Hannun Tinubu Na Da Damar Yin Korafi, APC

Fusatattun Yan Takarar da Suka Sha Kaye Hannun Tinubu Na Da Damar Yin Korafi, APC

  • Jam’iyyar APC mai mulki ta aika gaggarumin sako ga fusatattun mambobinta da suka nemi takarar shugaban kasa amma suka sha kaye
  • A wata sanarwa daga kakakin jam’iyyar, Felix Morka, ya ce yan takarar na da ikon yin korafi, cewa jam’iyyar na kokarin sasanta su
  • Tun bayan da Tinubu ya lashe tikitin takarar jam’iyyar, wasu fusatattun jiga-jigan jam’iyyar sun yi tsit ba’a kara jin doriyarsu ba

Sakataren labarai na jam’iyyar APC na kasa, Felix Morka, ya bayyana cewa fusatattun yan takarar da har yanzu suke jin zafi sakamakon faduwa da suka yi a zaben fidda dan takarar shugaban kasa suna da yancin nuna fushinsu.

Hakan na zuwa ne duk da tabbacin da ya bayar cewa shugabancin APC na aiki tukuru don sasanta duk fusatattun mambobin da jiga-jigan jam’iyyar gabannin zaben 2023, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

PDP ga Shettima: Cutar Mantau Ke Damunka, Gidanku Yana Ci da Wuta, Ku Fara Magance shi

Jiga-jigan APC
Fusatattun Yan Takarar da Suka Sha Kaye Hannun Tinubu Na Da Damar Yin Korafi, APC Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Morka ya yi jawabin ne lokacin da ya bayyana a shirin ‘Talk Point’ na Lagos Television a ranar Laraba, 2 ga watan Nuwamba.

Tinubu ya samu kuri’u 1,271 a zaben fidda gwanin da ya gabata inda ya lashe tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar mai mulki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kayar da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi; mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo da wasu yan takara 11 a babban taron jam’iyyar da aka yi a Abuja.

Osinbajo wanda basa ga maciji da ubangidan nasa ya nesanta kansa daga takarar shugabancin Tinubu.

Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, shima dan takara ne da ya haddasa cece-kuce bayan ya yi zargin cewa an baiwa deleget da suka kada kuri’u a zaben fidda gwanin cin hanci don sauya sakamakon.

Punch ta kuma rahoto cewa da yake martani ga zargin rikicin da halin ko-inkula da fusatattun mambobin ke yiwa kamfen din Tinubu, Morka ya ce jam’iyyar bata yi kasa a gwiwa ba a kokarinta na sasanta duk bangarorin kafin zaben 2023.

Kara karanta wannan

Kano: APC Ka Iya Shan Kaye a Zaben 2023, Doguwa Ya Magantu Bayan Barkewar Sabon Rikici

Ya ce:

“Bani da masaniya kan kowani rikici, balle ace mai sanyi ko mai zafi. Mutane sun shiga zaben fidda gwani don fafatawa da nufin yin nasara. A karshe, Asiwaju yayi nasara kuma ina ganin kowani dan takara na da yanci idan suka yanke shawarar kin amincewa da abun da basu yi nasara a kai ba.
“Muna aiki a cikin gida don magance matsalar da muke da shi daga wasu mambobi da suka fusata. Muna aiki tukuru don hada kansu.

Morka ya ce sabanin jita-jitan da ke yawo cewa jam’iyyar mai milk bata shirya ma zaben 2023 ba, tattaunawar da Tinubu ke ci gaba da yi da masu ruwa da tsaki ya isa hujja cewa sun shirya fiye da tunani.

Gwamna Ganduje Ya Roki Al'ummar Hausawa Su Taimaka Su Zabi Tinubu/Shettima a 2023

A gefe guda, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci al’ummar Hausa-Fulani mazauna jihar Kano da su marawa dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu da mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima baya a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Ana Wata Ga Wata: Ma'aikatan APC Sun Barke da Zanga-Zanga Kan Hakkinsu, Sun Nemi A Binciki Adamu

Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin wata ziyara da ya kaiwa al’ummar arewa a Alaba Rago da ke yankin Ojo na jihar, jaridar Punch ta rahoto. Ya kuma samu rakiyar Shettima da gwamnan jihar Lagas, Babajide Sanwo-Olu.

A nashi jawabin, Shettima ya bayyana cewa zaben 2023 lokaci ne da za a sakawa Tinubu a arewa, duba ga cewar ya marawa yan takara daga arewa baya a zabukan kasar na baya, rahoton TheCable.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng