2023: Abu Ne Mai Wahala Mu Iya Gamsar da Mutane PDP Zata Ceto Najeriya, Wike
- Gwamnan jihar Ribas yace abu ne mai wahala a yanzun su iya fahimtar da mutane cewa PDP ta shirya ceto Najeriya
- Wike da wasu gwamnonin PDP hudu sun ja daga sun jaddada cewa wajibi ne shugaban jam'iyya na ƙasa ya yi murabus
- Ayu ya tsaya kan bakarsa ta cewa ba zai bar mukaminsa ba domin an zaɓe shi ne ya yi wa'adin shekaru hudu
Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, yace abu ne mai wahala su iya gamsar da 'yan Najeriya har su yarda cewa jam'iyyar PDP zata iya ceto ƙasar nan idan ta koma mulki.
Wike yace yadda ake ƙasƙantar da kananan ƙalbilu a Najeriya na ɗaya daga cikin abubuwan da suka ƙara jefa ƙasar cikin kalubale, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Yace lamarin na ƙara zama, "Abu mai matukar wahala," iya gamsar da yan Najeriya cewa jam'iyyar PDP zata iya tsamo ƙasar nan daga waɗan nan matsaloli.
Gwamna Wike ya yi wannan furucin ne ranar Talata a Patakwal, jihar Ribas lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin jaridar New Telegraph.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Matsalolin ƙasar nan a yanzun ba wai yan bindiga ne ko masu garkuwa kaɗai ba, ɗaya daga batutuwan da suka shafi tsaro shi ne lamarin jefar da wasu."
"Ba zan gajiya ba wurin faɗa wa mutanen mu ko waɗanda ke ganin su ke da rinjaye cewa kuna bukatar zaman lafiya kafin ku iya jagorantar waɗanda basu da yawa."
"Idan babu zaman lafiya, lallai abun zai yi matukar wahala," inji Wike.
'Dole a samu dai-daito tsakanin kowane yanki'
Wike da wasu makusantansa na ci gaba da matsa lamba kan wajibi shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, yayi murabus domin ɗan kudu ya maye gurbinsa, hakan zai kawo dai-daito a jam'iyyar.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Mista Ayu da ɗan takarar shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, dukkansu sun fito ke daga yankin arewacin Najeriya.
Ayu ya jaddada cewa ba zai yi murabus ba. Ko a baya-bayan nan Ayu yace yana da karfin ikon soke tikitin takarar makiyansa kamar gwamna Ortom na jihar Benuwai.
A wani labarin kuma kun ji cewa Shugabannin PDP Sun Hargitse Bayan Wani Gwamna Ya Ayyana Goyon Bayan Tinubu a Fili
Abubuwan sun kara dagule wa a jam'iyyar PDP bayan kalaman gwamnan Oyo, Seyi Makinde, wanda ya nuna zai mara wa Tinubu baya.
Wata majiya tace babu wani cikakken mamban PDP mai kishi da zai nuna murna kan yadda abubuwa ke tafiya.
Asali: Legit.ng